Category: Politics
A Karon Farko Ganduje Ya Amince da Sanusi a Matsayin Sarki
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata ya fito fili ya amince da Alhaji Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano. Ganduje ya nuna wannan amincewa ne yayin bikin rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano. A…
Mambobin Majalisar Wakilai 17 Sun Fice daga ADC zuwa NDC
Akalla mambobi 17 na Majalisar Wakilai ta Tarayya sun fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa Nigerian Democratic Congress (NDC). An sanar da ficewar tasu ne a zauren majalisar yayin zaman majalisa na ranar Talata. Haka kuma, an sanar da ficewar dan majalisa Leke Abejide daga jam’iyyar ADC zuwa All Progressives Congress (APC). Daga…
Neman Wa’adi na Uku: Kaiama Sun ki Amincewa da Sanata Sadiq Umar
Wasu fitattun masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Kaiama da ke yankin Kwara ta Arewa sun fito fili sun soki Sanata Sadiq Umar bisa abin da suka bayyana a matsayin yunkurinsa na neman wa’adi na uku a majalisar dattawa, wanda suka ce ya sabawa tsohuwar yarjejeniyar rabon kujerar siyasa a yankin. Rahotanni sun bayyana…
Zaben 2027: Anas Galadima ya Shiga Takarar Kujerar Majalisar Wakilai
Wani kwararren ma’aikacin kafofin watsa labarai, sadarwa da manufofin jama’a, Anas Adamu Galadima, wanda aka fi sani da Zam-Zam, ya shiga takarar jam’iyyar APC domin neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Baruten–Kaiama. Galadima ya shiga takarar ne bayan ya sayi fom ɗin neman takara da kuma na bayyana sha’awa na jam’iyyar APC….
2027: Zan Tsaya Takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP – Mailantarki
Tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Gombe, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Mailantarki, wanda ya kasance ɗan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen 2023, ya miƙa takardar bayyana aniyarsa a sakatariyar PDP ta jiha da ke Gombe a…
ADC ta Ayyana Sayar da Fom ɗin Takarar Shugaban Ƙasa Naira Miliyan 100
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na shekarar 2026, inda ta sanya ranar 25 ga Mayu, 2026, a matsayin ranar zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, tare da kayyade farashin fom ɗin takarar shugaban ƙasa a Naira miliyan 100. A cikin wata sanarwa da mai magana da…
Zaben 2027: APC ta Sake Ɗaga Sayar da Fom Zuwa Ranar Laraba
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da sake tsawaita wa’adin sayarwa da kuma mika fom na tsayawa takara ga masu neman mukamai gabanin zaɓen 2027. A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar ranar Talata a Abuja, jam’iyyar ta ce sabon sauyin ya kuma shafi jadawalin tantance ‘yan takara, yayin da take ci…
Obi, Kwankwaso sun Fice Daga Jam’iyyar ADC Zuwa NDC
Bayan makonni ana ta hasashe kan makomarsu ta siyasa sakamakon rikicin da ke addabar jam’iyyar ADC, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, sun sanar da komawarsu jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a hukumance. Manyan ‘yan siyasar biyu sun bayyana wannan mataki ne…
Jamilu Gwamna ya zama ɗan takarar APC ta hanyar yarjejeniya a Gombe
Jamilu Isyaku Gwamna ya zama ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta hanyar yarjejeniya domin zaɓen gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027. An cimma wannan matsaya ne a ranar Lahadi yayin wani faɗaɗɗen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun…
2027: Zaben Bola Ahmed Tinubu na iya kawo karshen Najeriya — Hakeem Baba Ahmed
Shugaban jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) na kasa, Hakeem Baba Ahmed, ya gargadi cewa sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a 2027 na iya jefa Najeriya cikin matsananciyar barazana, idan halin da ake ciki a yanzu ya ci gaba. A wata hira da ya yi da jaridar Nigerian Tribune, Baba Ahmed ya…

