Zaben 2027: Anas Galadima ya Shiga Takarar Kujerar Majalisar Wakilai

Anas Zam Zam dan takarar Majalisar Wakilai karkashin jam’iyyar APC

Wani kwararren ma’aikacin kafofin watsa labarai, sadarwa da manufofin jama’a, Anas Adamu Galadima, wanda aka fi sani da Zam-Zam, ya shiga takarar jam’iyyar APC domin neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Baruten–Kaiama.

Galadima ya shiga takarar ne bayan ya sayi fom ɗin neman takara da kuma na bayyana sha’awa na jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan shigarsa takarar, Galadima ya nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar yankin, raunin wakilcin tarayya, da kuma rashin ingantattun hanyoyin sufuri a wasu sassan mazabar.

Ya bayyana cewa rashin tsaro, ƙarancin hanyoyin mota, da kuma rashin wadatattun damammakin tattalin arziki na ci gaba da shafar rayuwar al’umma, inda ya ce lamarin na bukatar wakilci mai ƙarfi da tsari a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

A cewarsa, Baruten–Kaiama na bukatar wakili da zai iya yin ingantaccen hulɗa da hukumomin tarayya domin jawo hankalin gwamnati kan ci gaban yankin.

Galadima ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi, zai yi amfani da kwarewarsa da kuma hanyoyin hulɗarsa na siyasa wajen jawo ayyukan gwamnatin tarayya, matakan tsaro, da shirye-shiryen ci gaba da za su inganta ababen more rayuwa, habaka tattalin arziki, da walwalar jama’a.

Ya kuma bayyana cewa zai yi aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, matasa da mata, da kuma hukumomin gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma ci gaba mai ɗorewa.

Dan takarar na APC ya kuma yabawa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa abin da ya kira ci gaban da gwamnatin sa ke aiwatarwa a Baruten da Kaiama, yana mai cewa gwamnatin ta yi manyan ayyuka a ƙananan hukumomin biyu.

Ya ce, “Tun bayan 1999 babu gwamnatin da ta bai wa Baruten da Kaiama kulawa ta musamman kamar wannan gwamnati.”

A baya, ya yi aiki da kamfanin Media Trust, masu buga jaridun Daily Trust, inda ya fara aiki a matsayin ɗan jarida da mai bincike har ya kai matsayin Editan Kasuwanci, kafin daga bisani ya shiga fannin banki da sadarwa.

Haka kuma, ya halarci wasu manyan shirye-shiryen horo a Makarantar Gwamnati ta Harvard Kennedy School, inda ya mayar da hankali kan tsarin dokoki, gyaran shugabanci, da kimanta shirye-shirye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *