Trends

Kotu Ta Soke Hukuncin da Ya Umarci INEC Ta Yi Wa NDC Rajista

Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, a ranar Juma’a ta soke hukuncinta na baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Mai shari’a Isah Dashen, wanda ya jagoranci shari’ar, ya ce dole ne a bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar gabatar da hujjojinsu kafin a yanke hukunci kan shari’ar.

Kotun ta amince da ƙorafin da jam’iyyar Peace Movement Party (PMP) ta shigar, tana mai cewa jam’iyyar na da muhimmiyar rawa a cikin shari’ar kuma ya kamata a saurare ta.

Mai shari’ar ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke a baya ya saɓa wa kundin tsarin mulki domin an yanke shi ba tare da an saurari dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba.

Ya ƙara da cewa hakan ya sa dukkan matakan da aka ɗauka a wancan hukuncin suka zama marasa inganci.

Kotun ta kuma umarci a mayar da al’amura yadda suke kafin hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, har sai an kammala sauraron ainihin shari’ar.

Mai shari’a Dashen ya kuma lura cewa an ɓoye wasu muhimman bayanai a shari’ar da ta gabata, lamarin da ya sa ya dace a soke hukuncin.

Saboda haka, kotun ta ba da umarnin a sake fara sauraron shari’ar tun daga farko, tare da haɗa INEC, PMP da NDC a matsayin ɓangarorin da ke cikin ƙarar.

Lauyan PMP, Chikezie Ekeocha, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyar ta garzaya kotu ne bayan ta gano cewa NDC ta yi amfani da tambarin da PMP ta riga ta miƙa wa INEC kafin fara shari’ar.

A cewarsa, kotun ta amince cewa an tauye haƙƙin PMP, saboda haka ta soke hukuncin da aka yanke a baya.

Ya ce kotun ta umarci a mayar da dukkan ɓangarorin zuwa matsayin da suke kafin hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, tare da umartar masu ƙarar su haɗa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa domin tabbatar da adalci.

Ekeocha ya bayyana cewa hukuncin na nufin dukkan matakan da INEC ta ɗauka bisa umarnin hukuncin da aka soke sun zama babu inganci.

Ya ce hakan ya haɗa da amincewa da NDC a matsayin jam’iyyar siyasa, ba ta takardar rajista, saka sunanta cikin bayanan INEC da kuma duk wani mataki na sanya ta cikin takardun zaɓe, har sai an yanke hukunci a kan ainihin shari’ar.

Sai dai ya jaddada cewa har yanzu ba a yanke hukunci kan ainihin shari’ar ba, domin kotun ta soke hukuncin da ta yanke a baya ne kawai tare da umartar a haɗa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa kafin a sake yanke sabon hukunci.

Labari NAN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *