Category: Politics
Peter Obi: Wataƙila Ba Zan Kai Ga Zaɓen 2027 Ba, Za Su Iya Kashe Ni
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa wataƙila ba zai kai ga shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, yana mai zargin cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kawo masa cikas tare da matsa wa ‘yan adawa lamba. Obi ya bayyana hakan ne a wata…
Zaɓen 2027: Akwai Sabuwar Yunkurin Hana ADC Shiga
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wata sabuwar makarkashiya da ake ƙullawa domin hana jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) shiga babban zaɓen shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu,…
Kotu Ta Soke Hukuncin da Ya Umarci INEC Ta Yi Wa NDC Rajista
Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, a ranar Juma’a ta soke hukuncinta na baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) rajista a matsayin jam’iyyar siyasa. Mai shari’a Isah Dashen, wanda ya jagoranci shari’ar, ya ce dole ne a bai wa…
Gombe 2027: PDP ta Bai wa Pantami Takardar Takara
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bai wa Farfesa Isa Ali Pantami, CON, Takardar Tabbatar da Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Gombe, wanda ke tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2027. An gudanar da bikin miƙa takardar ne a ranar Laraba yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar…
Kotu Ta Umarci INEC Ta Cire Rajistar ADC Da Sauran Jam’iyyu Hudu
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyu hudu bisa gazawarsu wajen cika sharuddan kundin tsarin mulki da dokokin kasa suka gindaya ga jam’iyyun siyasa. Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar…
Zaɓen 2027: Atiku Ya Zabi Amaechi a Matsayin Mataimakin sa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya zabi tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Amaechi, a matsayin abokin takararsa na mataimakin shugaban kasa. Wata majiya ta kusa da Amaechi da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da hakan, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Rivers na wa’adi biyu ya amince…
Majalisar Wakilai Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi
Majalisar Wakilai ta Tarayya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa tsarin ’yan sandan jihohi a faɗin Najeriya. ’Yan majalisar sun amince da kudirin ne a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan gudanar da ƙuri’a kan gyaran kundin tsarin mulkin da aka gabatar. Amincewar da majalisar ta yi da kudirin…
Zaɓen 2027: Obi Ya Zabi Kwankwaso A Matsayin Mataimakinsa a Tikitin NDC
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben shekarar 2027, Peter Obi, ya bayyana tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimakin shugaban kasa, lamarin da ake ganin zai kawo babban sauyi a siyasar Najeriya gabanin babban zaben kasa mai zuwa. Obi ya sanar da wannan mataki…
Jonathan Na Da ‘Yancin Tsayawa Takarar 2027 — Kotu
Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bai wa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027. Wata bangare ta jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ta bai wa Jonathan takardar rangwame a makon da ya gabata domin ya zama dan takarar shugaban kasa…
2027: Atiku Abubakar ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar ADC
Da yake bayyana sakamakon zaɓen a sakatariyar jam’iyyar da ke Sokoto, jami’in tattara sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jihar, Farfesa Aminu Abubakar, ya ce an kaɗa ƙuri’u 69,434 daga cikin masu rajista 69,871. A cewarsa, Atiku ya samu ƙuri’u 68,823 inda ya kayar da sauran masu neman takarar a zaɓen. Alhaji Muhammad…

