Peter Obi: Wataƙila Ba Zan Kai Ga Zaɓen 2027 Ba, Za Su Iya Kashe Ni

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa wataƙila ba zai kai ga shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, yana mai zargin cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kawo masa cikas tare da matsa wa ‘yan adawa lamba.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin With Chude, wanda fitaccen mai gabatar da shirye-shirye Chude Jideonwo ke gudanarwa. An wallafa wani ɓangare na hirar a shafin X na Chude a ranar Laraba.

Da yake amsa tambaya kan yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce irin matsin lambar da yake fuskanta ya kai matsayin da ba zai iya tabbatar da cewa zai kasance da rai zuwa lokacin zaɓen ba.

Ya ce, “Ba wai batun zama ɗan takara kawai ba ne. Wataƙila ma ba zan kasance da rai ba. Gaskiya nake faɗa muku. Duk abin da nake yi, wannan gwamnati tana kawo masa cikas da gangan. Akwai yiwuwar ma idan suka samu dama, ba zan kasance da rai ba.”

Sai dai Obi ya jaddada cewa ba ya zargin wani mutum kai tsaye, amma ya ce abubuwan da yake fuskanta na nuna akwai yunƙurin hana shi gudanar da harkokinsa yadda ya kamata.

Ya ce, “Ba zargi nake yi ba. Na san abin da nake fuskanta. Kowace rana ana kawo mini cikas. Abubuwan da ya kamata su zama na yau da kullum ba haka suke ba yanzu. Ba za su fito su ce su ne suke aikata hakan ba, amma ana iya ganin tasirinsu a kusan komai.”

Da aka tambaye shi ko yana ganin gwamnati na kai masa hari ne kai tsaye, Obi ya ce ba shi kaɗai ake yi wa hakan ba, domin a cewarsa ana matsa wa dukkan ‘yan adawa lamba.

Ya ƙara da cewa, “Ana kai wa duk wanda ke adawa hari. Ni ma ana kai mini hari kai tsaye. Har ma abubuwan da ya kamata gwamnati ta samar mini da su bisa haƙƙina ba a ba ni.”

Obi ya kawo misalin wani lamari da ya ce ya faru da shi a filin jirgin sama, inda ya yi zargin cewa jami’an filin sun kulle motarsa, yayin da suka bar motocin wasu ba tare da sun taɓa su ba.

A cewarsa, wasu mutane ma sun fara jin tsoron nuna suna tare da shi saboda fargabar abin da ka iya biyo baya. Ya ce wasu da suka san shi a filin jirgin sama kan guji gaishe shi, yayin da wasu masu gayyatarsa bukukuwan iyali kan roƙe shi kada ya halarta saboda tsoron jawo musu matsala.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Gwamnatin Tarayya ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen da Peter Obi ya yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *