Ambaliyar Ruwa YaYi Barna a Wasu Yankunan Jihar Kano
Ambaliyar ruwa ta fara ɓarna a wasu yankuna na arewacin Najeriya bayan faɗuwar damunar bana, inda a ƙarshen mako ruwan sama ya yi gagarumar ɓarna a wasu sassa na tsakar birnin Kano ciki har da ƙaramar hukumar Dala. Masana sun yi gargaɗi kan yiwuwar ambaliyar ta zarta wadda aka gani a bara. Tuni dai mahukuntan…

