Trends

Ambaliyar Ruwa YaYi Barna a Wasu Yankunan Jihar Kano

Ambaliyar ruwa ta fara ɓarna a wasu yankuna na arewacin Najeriya bayan faɗuwar damunar bana, inda a ƙarshen mako ruwan sama ya yi gagarumar ɓarna a wasu sassa na tsakar birnin Kano ciki har da ƙaramar hukumar Dala.

Masana sun yi gargaɗi kan yiwuwar ambaliyar ta zarta wadda aka gani a bara.

Tuni dai mahukuntan jihar suka ɗora alhakin ambaliyar ruwan kan matsalar rashin yashe magudanan ruwa, baya ga tara bola ko datti a wuraren da basu kamata ba.

Tun gabanin faɗuwar damuna masana sun yi gargaɗi kan yiwuwar fuskantar ambaliyar a wasu sassa na Najeriya ciki har da jihar Kano, gargadin da ya sanya bayar da shawarwarin yashe magudunan ruwa da ɗaukar sauran matakan da za su daƙile ambaliyar.

Ko a bara sai da ambaliyar ta yi mummunar ɓarna a sassan jihar Kano baya ga haddasa asara musamman ga manoma da ƴan kasuwa dama ɗaiɗaikun jama’a.