Yawan danyen man da Najeriya ke samarwa ya karu zuwa ganguna miliyan 1.53 a rana (mbpd) a watan Mayun 2026, wanda shi ne mafi girman adadi da aka samu tun watan Yulin 2025, a cewar sabon rahoton Kasuwar Mai na Watan-wata na OPEC.
Adadin ya nuna karin ganguna 41,000 a rana idan aka kwatanta da ganguna miliyan 1.489 da aka samar a watan Afrilu, lamarin da ya sa Najeriya ta sake wuce adadin da OPEC ta ware mata karo na farko cikin kusan shekara guda, tare da kara hasashen samun karin kudaden shiga.
OPEC ta bayyana cewa karuwar samar da man a Najeriya ta zo ne duk da raguwar da aka samu a wasu kasashen kungiyar Haɗin Gwiwar Samar da Mai (DoC), lamarin da ya kara tabbatar da matsayinta a matsayin kasa mafi girma wajen samar da mai a nahiyar Afirka.
Rahoton ya nuna cewa samar da mai a Najeriya ya karu da kusan kashi 2.8 cikin 100 daga wata zuwa wata, inda ta zarce wasu kasashen yankin kamar Libya mai ganguna miliyan 1.30 a rana, Aljeriya mai ganguna 982,000, Congo mai ganguna 283,000 da Gabon mai ganguna 210,000 a rana.
Najeriya ta karshe wuce adadin da OPEC ta ware mata ne a watan Yulin 2025, lokacin da ta samar da matsakaicin ganguna miliyan 1.507 a rana. Matakan inganta tsaron bututun mai da kuma kara zuba jari a harkokin hakar mai sun taimaka wajen wannan farfadowa.
Duk da kalubalen satar mai, lalata bututun mai da karancin zuba jari, Najeriya ta ci gaba da rike matsayinta na jagora a bangaren mai da iskar gas a Afirka.
Gwamnatin tarayya ta sanya ganguna miliyan 2.6 a rana a matsayin manufar samar da mai ta shekarar 2026, sai dai ta gina kasafin kudinta ne bisa hasashen ganguna miliyan 1.8 a rana. Ci gaba da samun karin samar da mai na iya karfafa ajiyar kudaden kasar, rage matsin tattalin arziki da kuma kara shigar kudaden musayar kasashen waje.
A baya, Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NUPRC) ta bayyana cewa Najeriya ta samar da ganguna miliyan 28.5 kacal ga matatun mai na cikin gida a rubu’in farko na shekarar 2026, kasa sosai da ganguna miliyan 61.9 da aka ware, lamarin da ke nuna cewa har yanzu akwai gibin aiki duk da ci gaban da ake samu wajen samar da danyen mai.
