Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali a Najeriya NCoS reshen jihar Kano ta bayyana yadda fursunoni 58 suka zana jarabawar kammala Sakandire ta ƙasa NECO a shekarar nan.
Kakakin gidan gyaran halin na jihar Kano Musbahu Kofar-Nasarawa ya shaidawa manema labarai a jiya Lahadi cewa yanzu haka fursunonin waɗanda ke tsaka da wa’adinsu na zaman kaso, na ci gaba da zana jarabawar kamar sauran ɗaliban makarantu.
A cewar Musbahu Kofar-Nasarawa tun farko Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne ya biyawa fursunoni kuɗin zana jarabawar, wanda zai basu damar samun shaidar kammala Sakandire duk da kasancewarsu a gidan yari.
Hukumar kula da gidajen gyaran halin wadda ta bayyana matakin Gwamnan jihar a matsayin wani gagarumin ci gaba da zai inganta rayuwar fursunonin bayan kammala wa’adinsu na zaman yari.
A cewar hukumar matakin ya bayyana aniyar gwamnati ta inganta rayuwar fursunonin a ciki gidajen yari da kuma bayan fitowarsu, ta yadda za su iya samun damar ci gaba da karatu bayan fitarsu.
