Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sake fasalin haraji, kuɗaɗen lasisi da sauran caji sama da 270 da ake karɓa a fannin mai da iskar gas na Najeriya, inda ta ɗauki kamfanin PwC domin gudanar da bincike da kwatanta tsarin harajin ƙasar da na sauran ƙasashen da ke hako mai.
Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur (Mai), Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron NOG Energy Week 2026 da aka gudanar a Abuja, bayan korafe-korafen da kamfanonin cikin gida masu hako mai suka yi kan yawaitar haraji da caje.
Shugaban Independent Petroleum Producers Group (IPPG), Adegbite Falade, ya bayyana cewa fannin mai na Najeriya na daga cikin waɗanda ake karɓar haraji mafi yawa a duniya, yana mai gargadin cewa tarin waɗannan caje na rage ƙarfin gasa tare da hana sabbin masu zuba jari shiga fannin.
Lokpobiri ya amince cewa korafe-korafen na da tushe, yana cewa akwai fiye da haraji da kuɗaɗe 270 a wannan fanni, amma ya jaddada cewa gwamnati na ɗaukar matakan magance matsalar.
Ya ce duk da cewa wasu daga cikin kuɗaɗen ba su da yawa, tsarin biyan su na buƙatar takardu masu yawa, wanda ke tilasta wa kamfanoni sarrafa daruruwan takardun biyan kuɗi.
Ministan ya ba da shawarar a haɗa waɗannan kuɗaɗe wuri guda, domin kamfanoni su rika biyan su lokaci ɗaya maimakon fitar da takardun biyan kuɗi sama da 270.
A cewarsa, binciken da PwC za ta gudanar zai kwatanta tsarin kuɗaɗen da ake karɓa a Najeriya da na sauran ƙasashen da ke hako mai, domin taimakawa gwamnati wajen yin gyare-gyaren da za su ƙara wa fannin ƙarfin gasa a duniya.
Shi ma Falade ya yi gargadin cewa yawaitar haraji da caje na rage tasirin sauye-sauyen da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA) ta kawo, musamman ga ƙananan kamfanonin hako mai da kuma tsofaffin rijiyoyin mai.
Ya buƙaci gwamnati ta haɗa caje da haraji tsakanin hukumomi daban-daban domin kauce wa maimaitawa tare da ƙara gaskiya da sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci.
Lokpobiri ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da niyyar magance matsalolin da suka shafi masana’antar, yana mai cewa wannan bincike zai taimaka wajen warware batun gaba ɗaya.





