Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC Limited, ya sanar da cewa ya rage kuɗaɗen gudanar da ayyukansa da dala biliyan 3.4, sakamakon sake fasalin kwangiloli da inganta yadda ake gudanar da ayyuka, abin da ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da ya samu tun bayan da ya koma kamfani mai cin gashin kansa na kasuwanci.
Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, Bashir Bayo Ojulari, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton cikar shekara guda na ayyukan NNPC a taron NOG Energy Week karo na 25 da aka gudanar a Abuja.
Ojulari ya ce an samu wannan tanadin kuɗi ba tare da rage ayyukan kamfanin ba, yana mai cewa inganta aiki da amfani da albarkatu yadda ya kamata ne ginshiƙin dabarun NNPC, ba ƙara kashe kuɗi ba.
Ya ce, “Waɗannan ba lambobi kaɗai ba ne. Suna nuna cewa ƙwarewar gudanar da aiki, ingantaccen tsarin kasuwanci da sauye-sauyen da aka aiwatar na iya ƙara yawan samar da mai, rage kashe kuɗi da kuma ƙara kuɗaɗen shiga ga ƙasa a lokaci guda.”
Rahoton ya nuna cewa yawan ɗanyen man da aka samar ya ƙaru da kashi 6 cikin ɗari, inda ya kai gangar mai miliyan 569.7, yayin da samar da iskar gas ya ƙaru da kashi 8.1 cikin ɗari, zuwa ƙafar ƙubi biliyan 2,576.
Haka kuma, kuɗaɗen da kamfanin ya tura wa gwamnati sun ƙaru da kashi 21.8 cikin ɗari, inda suka kai naira tiriliyan 19.5.
A cewar NNPC, yawan ɗanyen man da Najeriya ke samarwa yanzu ya kai gangar mai miliyan 1.71 a rana, wanda shi ne mafi girma cikin shekaru biyar da suka gabata. Sashen bincike da hako mai na NNPC kuwa ya kafa sabon tarihi da samar da gangar mai 365,000 a rana.
Kamfanin ya ce yana da burin kai samar da ɗanyen mai zuwa gangar mai miliyan 2 a rana nan da shekarar 2027, sannan zuwa gangar mai miliyan 3 a rana nan da shekarar 2030. Haka kuma yana son ƙara samar da iskar gas zuwa ƙafar ƙubi biliyan 12 a rana kafin shekarar 2030.
Ojulari ya kuma bayyana cewa an inganta amincin kayayyakin more rayuwa, inda manyan bututun jigilar ɗanyen mai ke aiki da cikakken ƙarfin aiki na kashi 100 cikin ɗari, yayin da tashoshin fitar da ɗanyen mai suka kai matakin dawo da aiki na kashi 98 cikin ɗari, idan aka kwatanta da kusan rashin aiki a tashar Bonny a shekarar 2022.
Ya kuma sanar da rattaba hannu kan manyan yarjejeniyoyin saye da sayar da iskar gas na dogon lokaci, domin samar da iskar gas ga masana’antar LNG da kasuwar cikin gida, waɗanda ake sa ran za su jawo saka hannun jari sama da dala biliyan 20.
Rahoton ya kuma ambaci matakan ƙara gaskiya da riƙon amana, ciki har da dawo da aika kuɗaɗen shiga ga gwamnati a kowane wata, gudanar da taron bayyana ribar kamfani, da kuma fitar da rahotannin ayyuka akai-akai.
Da yake magana kan makomar harkar makamashi a nahiyar Afirka, Ojulari ya buƙaci ƙasashen nahiyar su ƙarfafa haɗin gwiwa, yana mai cewa makomar makamashin Afirka ba za ta dogara ga albarkatun da ke ƙarƙashin ƙasa kaɗai ba, har ma da ingancin haɗin gwiwar da ƙasashen nahiyar za su gina a tsakaninsu.





