Mashigar Hormuz: Farashin Danyen Mai ya Tashi da Kashi 2% Bayan Hare-haren Jiragen Ruwa

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ƙaru da fiye da kashi 2 cikin ɗari a ranar Talata, bayan hare-haren da aka kai wa jiragen ruwa na kasuwanci a kusa da mashigar ruwan Hormuz, lamarin da ya sake tayar da fargabar katsewar isar da mai ta ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar makamashi a duniya.

Rahoton Oilprice.com ya nuna cewa farashin ɗanyen man Brent ya haura zuwa dala 74 kan kowace ganga, yayin da ɗanyen man WTI ya ƙaru da dala 1.73, wanda ya kai kashi 2.52 cikin ɗari, zuwa dala 70.28 kan kowace ganga, yayin da masu ciniki suka fara la’akari da ƙarin haɗarin rikicin siyasa.

Rahotanni sun ce wani jirgin dakon iskar gas na Qatar (LNG) da kuma wani jirgin dakon ɗanyen mai mai tutar Saudi Arabiya sun samu ɓarna bayan da ake zargin dakarun Iran Revolutionary Guards sun harba makamai masu linzami kan jiragen da ke bi ta mashigar Hormuz.

Ƙasar Qatar ta ɗora alhakin harin kan Iran, sai dai gwamnatin Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan zargin ba.

Wannan lamari ya sake ƙara fargaba game da tsaron mashigar Hormuz, wadda kafin yaƙin Amurka da Iran da ya ɓarke a watan Fabrairu, take ɗaukar kusan kashi 20 cikin ɗari na jigilar ɗanyen mai da iskar gas (LNG) na duniya. Masana sun ce duk wata tangarda a wannan hanya na iya rage wadatar mai a kasuwannin duniya tare da ƙara tsadar makamashi.

Masana harkokin makamashi sun bayyana cewa hare-haren sun sake ƙara haɗarin rikicin siyasa a kasuwar mai.

Shugaban kamfanin Lipow Oil Associates, Andy Lipow, ya ce masu jigilar kaya za su sake nazarin haɗarin amfani da wannan mashigar ruwa.

Ya ce, “A bayyane yake cewa haɗarin har yanzu yana nan.”

A halin da ake ciki, rikicin diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka na ci gaba da ƙamari, inda Iran ta yi gargadin cewa tattaunawa da Washington za ta rushe idan Amurka ta ci gaba da yin barazana.

Shi ma shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi alkawarin cewa zai “kammala aikin” matuƙar ba a cimma yarjejeniya ba.

Duk da tashin farashin man, bankin Société Générale ya yi hasashen cewa kasuwar mai za ta sauya daga ƙarancin wadatar mai zuwa yalwar mai a ƙarshen shekarar 2026 da kuma cikin 2027.

Bankin ya rage hasashen farashin ɗanyen mai na ƙarshen shekarar 2026 zuwa dala 75 kan kowace ganga, maimakon dala 83, sannan ya rage matsakaicin hasashen shekarar 2027 zuwa dala 73, daga dala 79, tare da gargadin cewa kasuwar za ta ci gaba da fuskantar sauyin farashi.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Saudi Arabiya na duba yiwuwar faɗaɗa bututun jigilar mai zuwa gabar Tekun Bahar Maliya (Red Sea) domin rage dogaro da mashigar Hormuz.

A lokaci guda kuma, rundunar sojin Ukraine ta ce ta kai hare-haren jiragen sama marasa matuƙa kan wasu jiragen dakon mai na Rasha guda takwas da ake kira “shadow fleet”, abin da ya ƙara jefa kasuwar makamashi ta duniya cikin rashin tabbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *