UAE ta Ƙara Samar da Gangar Mai Miliyan 3.8 a Rana Bayan Ficewa daga OPEC+

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ƙara yawan hako ɗanyen mai zuwa gangar mai miliyan 3.8 a rana a watan Yuni, wanda shi ne mafi girman matakin da ƙasar ta kai tun watan Afrilun shekarar 2020, bayan ficewarta daga ƙungiyar OPEC+ domin kauce wa ƙa’idodin takaita yawan hako mai.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa fitar da ɗanyen mai na kamfanin ADNOC ta kai gangar mai miliyan 3.94 a rana, matakin da ya kusa kai wa tarihin da aka kafa a ƙarshen shekarar 2025.

Rahoton ya ce wannan ci gaba ya nuna cewa matakin da UAE ta ɗauka na ficewa daga OPEC+ a ranar 1 ga Mayu ya fara haifar mata da fa’ida, bayan an cire mata takunkumin iyakance yawan hako mai.

A lokacin rikicin yaƙin Iran a watan Mayu, yawan hako man UAE ya ragu zuwa gangar mai miliyan 2.11 a rana, amma saka hannun jarin da ƙasar ta yi wajen faɗaɗa ƙarfin hako mai ya ba ta damar farfaɗowa cikin sauri.

Sai dai Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta fitar da ƙididdiga mafi girma, inda ta ce UAE ta samar da gangar mai miliyan 2.8 a rana a watan Mayu, sannan ta kai miliyan 3.64 a rana tun watan Fabrairu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa kamfanin ADNOC na sayar da ɗanyen mai da rangwamen farashi, lamarin da ya jawo sabbin masu saye ciki har da ƙananan matatun mai na kasar Sin da kuma wasu matatun mai a jihar California ta Amurka, waɗanda suka shiga tayin sayen man kamfanin a karon farko.

‘Yan kasuwar mai sun ce rangwamen farashin ya sa ɗanyen man UAE ya fi iya gogayya da man Iran da na Rasha a kasuwa.

Ministan Makamashi na UAE, Suhail Al-Mazrouei, ya kare matakin ficewa daga OPEC+, yana cewa ƙasar na da alhakin samar wa masu zuba jari damar isar da mai zuwa kasuwannin duniya “ba tare da wani takurawa ba.”

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa farfaɗowar UAE ta zarce ta sauran manyan ƙasashen yankin Gulf. Jimillar fitar da mai daga Saudi Arabiya, UAE, Kuwait, Iraƙi da Iran ta kai kusan gangar mai miliyan 10 a rana a watan Yuni, daga miliyan 7 a watan Mayu, duk da cewa har yanzu ba ta kai gangar mai miliyan 16.5 a rana da aka fitar a irin wannan lokaci na bara ba.

A cewar rahoton, Saudi Arabiya ta fitar da gangar mai miliyan 4.32 a rana, Kuwait ta kai miliyan 1.65 a rana, yayin da Iraƙi ta fitar da gangar mai 780,000 a rana, wanda ya kai kusan kashi ɗaya cikin biyar na abin da take fitarwa kafin rikicin yankin.

Masana sun bayyana cewa duk da cewa ƙarin yawan man da UAE ke fitarwa ya rage fargabar ƙarancin mai a kasuwannin duniya, hakan na kuma haifar da damuwa kan yiwuwar samun cunkoson mai a kasuwa na ɗan lokaci, musamman bayan da ADNOC ta sayar da gangar mai miliyan 18 a sabon tayin da ta fitar.

Wata masaniya a kamfanin Sparta, June Goh, ta ce masu ƙananan matatun mai na kasar Sin na ci gaba da sayen mai daga UAE saboda rangwamen farashinsa, wanda ya sa yake gogayya da ɗanyen man Iran da na Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *