Sabbin bayanai daga Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa ’yan Najeriya na rike da Naira tiriliyan 5.19 a wajen tsarin bankuna zuwa watan Mayun 2026, lamarin da ke nuna cewa amfani da kuɗi a hannu na ci gaba da rinjaye duk da shekaru na ƙoƙarin bunƙasa biyan kuɗi ta hanyar zamani da faɗaɗa harkokin hada-hadar kuɗi.
Bayanan sun nuna cewa kuɗin da ke wajen bankuna ya ƙaru daga Naira tiriliyan 5.08 a watan Afrilu zuwa Naira tiriliyan 5.19 a watan Mayu, wanda ke nuna ƙarin Naira biliyan 109.34 ko kashi 2.15 cikin 100 a wata guda.
Idan aka kwatanta da watan Mayun 2025, adadin ya ƙaru da Naira biliyan 559.16, wanda ya kai kashi 12.07 cikin 100 a shekara guda.
Jimillar kuɗin da ke yawo a tattalin arziki ma ta ƙaru zuwa Naira tiriliyan 5.69 a watan Mayu. Daga cikin wannan adadi, kuɗin da ke wajen bankuna ya kai kashi 91.27 cikin 100, ma’ana fiye da Naira tara cikin kowace Naira goma na yawo ne a wajen hanyoyin bankuna na hukuma.
Duk da ci gaba da amfani da kuɗi a hannu, ajiyar kuɗaɗen bankuna a CBN ta ragu da Naira biliyan 841 a watan Mayu, inda ta sauka daga Naira tiriliyan 34.6 zuwa Naira tiriliyan 33.8. Hakan na nuna raguwar tanadin kuɗaɗen bankuna duk da karuwar kuɗin da ke yawo a hannun jama’a.
Sai dai idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, ajiyar bankunan ta ƙaru da Naira tiriliyan 2.9, wanda ya kai kashi 9.39 cikin 100.
Masana sun ce waɗannan alkaluma na nuna cewa sauyin Najeriya zuwa tattalin arzikin da ya fi dogaro da hanyoyin biyan kuɗi na zamani yana tafiya a hankali.
Duk da saurin bunƙasar biyan kuɗi kai tsaye, bankin waya, ayyukan fintech da kuma hanyoyin wakilan banki, har yanzu kuɗi a hannu ne ya fi rinjaye a harkokin kasuwancin dillalai, sufuri, kasuwancin da ba na hukuma ba da kuma ayyukan tattalin arziki a yankunan karkara.
A wajen ƙaddamar da Tsarin Biyan Kuɗi na Najeriya zuwa 2028 (Payment System Vision 2028), Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa manufar bankin ita ce rage yawan kuɗin da ke wajen bankuna zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 na jimillar kuɗin da ke yawo a ƙasar.
Ya ce daga cikin matakan da ake shirin ɗauka akwai samar da wuraren biyan kuɗi sama da miliyan 10 ta hanyar amfani da lambar QR da fasahar “tap-to-pay” a faɗin ƙasar.
Masana tattalin arziki sun ce ci gaba da amfani da kuɗi a hannu yana da nasaba da matsalolin amincewa da tsarin kuɗi, ƙarancin kayayyakin more rayuwa da kuma yadda tattalin arzikin da ba na hukuma ba ke ci gaba da dogaro da kuɗi a zahiri, duk da ƙoƙarin masu tsara manufofi na gina tsarin hada-hadar kuɗi mai amfani da fasaha kuma mai haɗa kowa da kowa.








