MAN ta Nuna Damuwa Bayan Bashin Masana’antu ya Ragu da Naira Tiriliyan 1.92

Kungiyar Masana’antun Najeriya (MAN) ta yi gargadin cewa masana’antun kasar na fuskantar karin matsin tattalin arziki bayan bashin da bankuna ke bai wa bangaren ya ragu da Naira tiriliyan 1.92.

A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan kungiyar, Segun Ajayi-Kadir, ya sanya wa hannu, MAN ta ce bashin da aka bai wa masana’antun ya sauka daga Naira tiriliyan 8.53 a watan Disamban 2024 zuwa Naira tiriliyan 6.61 a watan Disamban 2025, wanda ke nuna raguwar kashi 22.5 cikin 100.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan koma baya na nuna yadda yanayin kasuwanci ke kara tsananta ga masana’antun da tuni suke fama da tsadar makamashi, rashin daidaiton farashin canjin kudaden waje da kuma hauhawar kudin samar da kayayyaki.

MAN ta kuma nuna damuwa kan yadda kudin ruwa na rancen bankuna ke ci gaba da kasancewa mai tsada, inda matsakaicin kudin ruwa ga manyan kwastomomi ya kai kashi 27 cikin 100, yayin da mafi girman kudin ruwa ya kai kashi 35.6 cikin 100, duk da cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ci gaba da rike kudin ruwa na manufofinsa (MPR) a kashi 26.5 cikin 100.

Kungiyar ta ce babban abin da ke hana masana’antun samun damar cin gajiyar kudaden da ke cikin bankuna shi ne tsananin tsadar aro.

Yayin da bashin da aka bai wa bangaren masana’antu ya ragu sosai, bangaren mai da iskar gas ya samu Naira tiriliyan 10.59, yayin da bangaren hada-hadar kudi ya samu Naira tiriliyan 9.24, lamarin da ke nuna cewa bankuna na fifita bangarorin da ke samar da riba cikin gaggawa.

MAN ta danganta wannan matsala da tsauraran manufofin kudi, yawan kaso na ajiyar dole da bankuna ke ajiye wa CBN (CRR) wanda ya kai tsakanin kashi 45 zuwa 50 cikin 100, da kuma yadda bankuna ke kauce wa hadari wajen bayar da bashi.

Kungiyar ta kuma ce sharuddan jingina kadarori da samar da jarin kai sun hana kananan masana’antu damar samun tallafin kudi.

Haka kuma, MAN ta soki jinkirin aiwatar da Asusun Tallafawa Masana’antu na Naira tiriliyan 1 da Gwamnatin Tarayya ta yi alkawari karkashin Shirin Gaggauta Daidaitawa da Ci Gaba (ASAP), tana mai cewa kusan shekaru biyu kenan amma har yanzu masana’antun ba su samu damar cin gajiyar tallafin ba.

Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin samun bashi mai saukin ruwa zai iya rage yawan kayayyakin da masana’antu ke samarwa, hana sabbin zuba jari da kuma haifar da asarar ayyukan yi.

Ta kuma yi nuni da cewa manufofin bunkasa masana’antu na Najeriya na shekarar 2025 na iya fuskantar cikas idan kudin ruwa kan rance ya ci gaba da kasancewa sama da kashi 30 cikin 100.

A cewar MAN, raguwar samar da kayayyaki a cikin gida na iya kara tsananta hauhawar farashi da ke samo asali daga bangaren samarwa, kara dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje, tare da kara matsin lamba kan bukatar kudaden waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *