Kwamitin Ba da Matsayin Babban Lauyan Najeriya (LPPC) ya dakatar da matsayin Senior Advocate of Nigeria (SAN) na fitaccen lauya mai rajin kare kundin tsarin mulki, Mike Ozekhome, har sai an kammala shari’o’in ladabtarwa da ake yi masa.
An yanke wannan hukunci ne a taro na 173 na kwamitin da aka gudanar ranar 23 ga Yunin 2026.
A cikin wata sanarwa da Babban Magatakardan Kotun Koli kuma Sakataren LPPC, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu kuma aka fitar da ita a daren Laraba, kwamitin ya ce an amince da dakatarwar ne bisa tanadin Sashe na 26(6) na Ka’idojin Ba da Matsayin SAN.
Sanarwar ta ce, “Kwamitin Ba da Matsayin Babban Lauyan Najeriya (LPPC), a taronsa na 173 da aka gudanar ranar 23 ga Yuni, 2026, ya amince da dakatar da Chief Mike Ozekhome daga matsayin Senior Advocate of Nigeria.”
Kwamitin ya kara da cewa an dauki matakin ne har sai an kammala binciken ladabtarwa da ke gaban Kwamitin Ladabtarwa da Da’a na LPPC da kuma wasu shari’o’in da suke gudana.
A cewar LPPC, an dauki wannan mataki ne domin kare mutunci, daraja da martabar matsayin SAN yayin da ake nazarin batutuwan da ake zarginsa da su.
Kwamitin ya kuma umarci Ozekhome da ya daina bayyana kansa a matsayin Senior Advocate of Nigeria a lokacin da dakatarwar ke aiki.
LPPC ta jaddada kudurinta na tabbatar da bin mafi girman ka’idojin da’a, gaskiya da ladabtarwa a harkar shari’a, tare da tabbatar da cewa matsayin SAN na ci gaba da samun amincewa da girmamawa daga jama’a.
Dakatarwar na zuwa ne yayin da babban lauyan ke fuskantar wasu matsalolin shari’a a watannin baya-bayan nan.
A watan Janairu, Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) ta shigar da kara a kansa kan zarge-zargen damfara da kuma amfani da takardun bogi dangane da wata kadarar da ke lamba 79 Randall Avenue, Neasden, a birnin London na Birtaniya.
Daga baya, Babban Lauyan Tarayya ya karbi ragamar shari’ar, yayin da masu gabatar da kara suka yi zargin cewa an yi amfani da takardun bogi, ciki har da fasfo din Najeriya, wajen tabbatar da mallakar kadarar.
Rikicin kadarar da ke London ya jawo hankalin duniya bayan wata Kotun Kula da Harkokin Kadarori ta Birtaniya ta yi watsi da ikirarin da Ozekhome da wasu suka gabatar, inda ta ce akwai shaidun damfara, satar suna da kuma amfani da takardun bogi dangane da mallakar gidan.
A wani bangare kuma, a watan Maris, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace kadarar da ke London gaba daya tare da mika ta ga Gwamnatin Tarayya, bayan babu wani da ya samu nasarar tabbatar da mallakarta a gaban kotu.








