Neman Wa’adi na Uku: Kaiama Sun ki Amincewa da Sanata Sadiq Umar

Wasu fitattun masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Kaiama da ke yankin Kwara ta Arewa sun fito fili sun soki Sanata Sadiq Umar bisa abin da suka bayyana a matsayin yunkurinsa na neman wa’adi na uku a majalisar dattawa, wanda suka ce ya sabawa tsohuwar yarjejeniyar rabon kujerar siyasa a yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa Sanatan ya sayi fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara domin sake neman kujerar Sanata, duk da cewa akwai fahimtar cewa ya kamata kujerar ta koma bangaren masu magana da harshen Nupe a Kwara ta Arewa, bisa tsarin rabon kujera (zoning) da aka amince da shi.

A cikin wata sanarwa mai zafi da aka fitar karkashin sunan “Concerned Kaiama Stakeholders,” kungiyar ta zargi Sanata Umar da fifita bukatar kansa a kan muradun al’umma, tare da gargadin cewa irin wannan mataki na iya tayar da hankali da rikici a cikin daidaiton siyasar yankin Kwara ta Arewa.

A cewar masu ruwa da tsakin, yankin ya dade yana aiki da wata yarjejeniya ta fahimtar juna wadda ke bai wa kowace karamar hukuma damar rike kujerar Sanata na tsawon wa’adi biyu kacal kafin a mika ta ga wata karamar hukuma. Sun ce wannan tsari ya taimaka wajen tabbatar da adalci, hadin kai da zaman lafiya a yankin.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa cewa Sanata Umar ya ci gajiyar wannan tsarin ne wajen samun kujerarsa, abin da ma ya taba amincewa da shi a cikin littafinsa mai suna “How I Became a Senator in 30 Days,” amma yanzu ana zarginsa da kokarin yin watsi da wannan tsari. Sun bayyana wannan mataki a matsayin “babban karya amana” wanda ke jefa shakku kan nagartar shugabanci da mutunta yarjejeniyar al’umma.

“Idan da akwai bukatar sake duba wannan tsarin, hanya mafi dacewa ita ce tuntubar manyan mutane da masu ruwa da tsaki a fadin Kwara ta Arewa,” in ji sanarwar. “Duk wani mataki da aka dauka ba tare da tuntuba ba yana raunana tsarin da kuma hadin kan da aka gina tsawon shekaru.”

Masu ruwa da tsakin sun yi gargadin cewa watsi da wannan yarjejeniya na iya haifar da mummunan sakamako, ciki har da lalata amincewa tsakanin kananan hukumomi, bata sunan Kaiama a siyasa, da kuma haddasa rarrabuwar kawuna a yankin.

Sun kuma yi kira ga shugabannin siyasa, sarakuna da sauran masu fada a ji a Kaiama da su fito su yi magana domin tabbatar da cewa an kiyaye wannan tsarin da aka saba.

“Shiru a irin wannan lokaci na iya zama kamar amincewa da abin da ke faruwa,” in ji kungiyar, inda suka bukaci a dauki matakin gaggawa domin kare mutuncin tsarin siyasar yankin.

A karshe, sanarwar ta bukaci Sanata Umar da ya “sake tunani” tare da bin muradun al’umma da yankin Kwara ta Arewa baki daya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Sanata Sadiq Umar bai fitar da wata martani a bainar jama’a ba kan zargin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *