Mambobin Majalisar Wakilai 17 Sun Fice daga ADC zuwa NDC

Majalisar Dokoki Majalisar Dokoki

Akalla mambobi 17 na Majalisar Wakilai ta Tarayya sun fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa Nigerian Democratic Congress (NDC).

An sanar da ficewar tasu ne a zauren majalisar yayin zaman majalisa na ranar Talata. Haka kuma, an sanar da ficewar dan majalisa Leke Abejide daga jam’iyyar ADC zuwa All Progressives Congress (APC).

Daga cikin ‘yan majalisar da suka koma jam’iyyar NDC akwai Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi, Peter Aniekwe, Mukhtar Zakari, George Oluwande da kuma Munachim Umezuruike.

Sauran sun hada da Emeka Idu, Jesse Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene da Abdulhakeem Ado.

Ficewar wadannan ‘yan majalisa na nuni da sauyin siyasa a majalisar, lamarin da ka iya shafar daidaiton karfi tsakanin jam’iyyun siyasa a majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *