Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata ya fito fili ya amince da Alhaji Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano.
Ganduje ya nuna wannan amincewa ne yayin bikin rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano.
A cikin jawabinsa, tsohon gwamnan ya gaishe da Sanusi tare da kiransa da cikakken sarautarsa, matakin da ya jawo tafi da murna daga manyan baki da mahalarta taron.
Wannan ne karo na farko da Ganduje ya fito fili ya amince da Sanusi a wannan matsayi tun bayan rikicin da ya taba shiga tsakaninsu wanda ya yi fice a kafafen yada labarai.
A shekarar 2020, lokacin da yake gwamna, Ganduje ya tube Sanusi daga sarautar Sarkin Kano.
Sai dai daga bisani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maido da Sanusi kan karagar mulki, bayan ya cire Alhaji Aminu Ado Bayero wanda Ganduje ya nada a matsayin wanda zai maye gurbin Sanusi.
Duk da haka, Aminu Ado Bayero ya ki sauka daga mukaminsa, inda ake zargin yana samun goyon bayan Ganduje da kuma gwamnatin tarayya.
Lamarin ya dauki sabon salo ne bayan Gwamna Yusuf ya koma jam’iyyar APC watanni da suka gabata.
Haka kuma, an bai wa Sanusi damar gudanar da hawan Sallah (Durbar), sabanin baya inda ‘yan sanda suka gayyace shi kan rikicin da ya barke yayin hawan, wanda har aka dakatar da shi a wancan lokaci.
Labari: Daily Trust



