ADC ta Ayyana Sayar da Fom ɗin Takarar Shugaban Ƙasa Naira Miliyan 100

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na shekarar 2026, inda ta sanya ranar 25 ga Mayu, 2026, a matsayin ranar zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, tare da kayyade farashin fom ɗin takarar shugaban ƙasa a Naira miliyan 100.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce jadawalin ya ƙunshi ƙa’idoji da sharudda na zaɓen ‘yan takara gabanin babban zaɓen 2027, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da dimokuraɗiyya a cikin gida, tsari mai kyau da kuma bin dokar zaɓe.

Bisa jadawalin, an riga an fara tsarin, inda karɓar fom na neman takara ke gudana daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 4 ga Mayu, 2026.

Sayar da fom na tsayawa takara zai gudana daga ranar 5 zuwa 10 ga Mayu, yayin da za a karɓi cikakkun fom daga ranar 11 zuwa 13 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta ce za a gudanar da tantance masu neman takara daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu, sannan za a fitar da sakamakon tantancewar a ranar 17 ga Mayu.

Za a saurari ƙorafe-ƙorafen da suka taso daga tantancewar daga ranar 18 zuwa 19 ga Mayu, yayin da ake sa ran fitar da jerin sunayen waɗanda aka amince da su a ranar 20 ga Mayu.

Zaɓen fidda gwani na majalisun jihohi, na majalisar wakilai da na majalisar dattawa za su gudana lokaci guda a matakin mazabu a ranar 21 ga Mayu, 2026. Zaɓen gwamna zai biyo baya a ranar 22 ga Mayu, yayin da aka sanya zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a ranar 25 ga Mayu.

Jadawalin ya kuma tanadi taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) a ranar 26 ga Mayu, 2026, da kuma babban taron ƙasa na musamman a ranar 27 ga Mayu, inda za a amince da ‘yan takara na ƙarshe.

Dangane da kuɗin fom, ADC ta amince da tsarin kuɗi na musamman ga dukkan mukaman zaɓe.

Yayin da aka kayyade fom na shugaban ƙasa a Naira miliyan 100, na gwamna zai kai Naira miliyan 50, na majalisar dattawa Naira miliyan 20, na majalisar wakilai Naira miliyan 10, yayin da na majalisar dokokin jiha yake Naira miliyan 3.

Jam’iyyar ta sanar da rangwamen kashi 50 cikin 100 ga matasa, da kuma kashi 25 cikin 100 ga mata da masu nakasa.

ADC ta buƙaci duk masu neman takara, mambobi da masu ruwa da tsaki su bi jadawalin da ƙa’idojin da aka gindaya, tana mai jaddada kudurinta na samar da sahihin dandamali ga shugabanci nagari da rikon amana a zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *