Jamilu Gwamna ya zama ɗan takarar APC ta hanyar yarjejeniya a Gombe

Jamilu Isyaku Gwamna ya zama ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta hanyar yarjejeniya domin zaɓen gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027.

An cimma wannan matsaya ne a ranar Lahadi yayin wani faɗaɗɗen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun da farko ‘yan siyasa 11 sun nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Bisa ga jerin sunayen da sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar ta fitar, masu neman takarar sun haɗa da: Dr. Jamilu Isyaku Gwamna, Dr. Aminu Yuguda, Farfesa Isa Ali Pantami, Sanata Saidu Alkali, Alhaji Umaru Kwairanga (Sarkin Fulani), Injiniya Abubakar Bappah, Hon. Muhammad Gambo Magaji, Abubakar Sadiq Shu’aibu, Babban Whip na Majalisar Wakilai Usman Bello Kumo, tsohon Ministan Sufuri Injiniya Aliyu Muhammad (Combat).

Sai dai Sanata Alkali, Farfesa Pantami da Injiniya Aliyu Muhammad sun kaurace wa tarukan masu ruwa da tsakin da aka gudanar a daren Asabar da kuma yammacin Lahadi.

Taron ya kuma amince da ‘yan takarar yarjejeniya na kujerun sanatoci uku na jihar, da kujeru shida na Majalisar Wakilai, da kuma kujeru 24 na Majalisar Dokokin Jihar.

Jam’iyyar ta zaɓi Mohammed Jarman Deba a matsayin ɗan takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya, kujerar da a halin yanzu Sanata Muhammad Danjuma Goje ke riƙe da ita.

A yankin Sanatan Gombe ta Arewa kuwa, jam’iyyar ta zaɓi Gwamna Inuwa Yahaya ya fafata da Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo na jam’iyyar PDP.

Haka kuma a yankin Sanatan Gombe ta Kudu, an zaɓi Joseph Jerry Damara a matsayin ɗan takarar yarjejeniya, inda aka kauce wa zaɓen Sanata Antony Siyako Yaro mai ci, wanda kwanan nan ya koma jam’iyyar APC.

Dangane da kujerun Majalisar Wakilai shida, an zaɓi Usman Bello Kumo na mazabar Akko; Ali Isa JC na Balanga/Billiri; Jamilu Shabewa na Dukku, inda zai fafata da ɗan majalisa mai ci Abdullahi El-Rasheed.

Sauran sun haɗa da Sadam Bello Saleh na Gombe/Kwami/Funakaye; Fatima Binta Bello na Kaltungo/Shongom; da kuma Inuwa Garba na Yamaltu/Deba, wanda shi ma ɗan majalisa ne mai ci kuma ya koma APC kwanan nan.

A baya labarai ya bayyana cewa Gwamna Yahaya ya bayar da umarnin a sayi fom guda ɗaya kacal na takarar gwamna, uku na sanatoci da shida na Majalisar Wakilai, bisa tsarin yarjejeniya, inda duk masu neman takara suka amince za su mara wa duk wanda ya fito baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *