Ƙungiyar Pantamiyya Movement Brotherhood (PMB) ƙarƙashin jagorancin Ameer Sanusin Gombe, ɗaya daga cikin wakilan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami, ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC da kuma sauran ’yan takarar jam’iyyar da suka samu nasara a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a jihar Gombe.
Da yake jawabi, Sanusi Hamisu Usman wanda aka fi sani da Sanusin Gombe, ya ce nan ba da jimawa ba jagoran ƙungiyar Pantamiyya, Farfesa Isa Pantami, tare da mambobin zartarwar PMB za su fito fili su bayyana irin wannan goyon baya.
Ya bayyana cewa sun shawarci Pantami da ya ci gaba da mara wa jam’iyyar APC baya ta hanyoyi daban-daban, la’akari da matsayinsa a jam’iyyar a matsayin jagora ba kawai ɗan jam’iyya ba.
Sanusin Gombe ya ce duk da rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta a halin yanzu, ƙungiyar PMB ba ta goyon bayan duk wani yunƙuri da zai sa Isa Pantami ko mabiyansa su fice daga jam’iyyar APC.
Ya ƙara da cewa kowace jam’iyya a Najeriya na da nata ƙalubalen cikin gida, saboda haka suna ganin ya dace Pantami ya yi haƙuri tare da yin watsi da duk wata shawara da za ta iya sa shi barin jam’iyyar mai mulki.
A cewarsa, PMB na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da haɗin kai da cigaban jam’iyyar APC a jihar Gombe da ma ƙasa baki ɗaya.

