Hukumomin Saudiyya sun sanar cewa hudubar Arfa ta wannan shekarar a lokacin aikin Hajj za a fassara ta zuwa harsuna 35, sannan za a watsa ta ta kafafen dijital da tashoshin da ke da alaƙa da ita.
Wannan shiri na nufin bai wa miliyoyin alhazai da Musulmi a fadin duniya damar bin hudubar a harsunansu na asali.
Hukumar Kula da Harkokin Addini a Masallacin Harami da Masallacin Annabi, Presidency of Religious Affairs at the Grand Mosque and the Prophet’s Mosque, ta ce fassarar za ta shafi manyan harsunan duniya da na yankuna daga Afirka, Asiya, Turai da sauran sassa na duniya.
Harsunan da aka amince da su sun hada da Ingilishi, Faransanci, Yarbanci, Hausa, Indonesiyanci, Urdu, Turkiyya, Farisanci, Sifaniyanci, Sinanci, Rashanci, Bengali, Hindi, Malay, Amharic, Swahili, Somali, Pashto, Punjabi, Tamil da Filipino.
Sauran harsunan sun hada da Bosniyanci, Jamusanci, Italiyanci, Fotugis, Swidish, Uzbek, Tajik, Nepali, Sinhala, Malayalam, Oromo, Tigrinya, Ugandan da Lithuanian.
Shugaban hukumar, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, Abdulrahman Al-Sudais, ya ce wannan shiri an tsara shi ne domin isar da saƙon hudubar na ruhaniya da kuma koyarwar Musulunci na matsakaiciya ga al’ummar duniya baki ɗaya.
Ya ce: “Aikin fassarar hudubar Arfa na daga cikin manyan shirye-shiryen hukumar da aka gina bisa kwarewar shekaru masu yawa. Yana bai wa Musulmi da ba sa jin Larabci damar amfana da saƙon ruhaniya da na jinƙai na hudubar.”
Al-Sudais ya ƙara da cewa hukumar ta tura kayan aiki na fasaha da kafafen watsa labarai tare da ƙwararrun ma’aikata domin tabbatar da cewa hudubar ta isa ga mutane mafi yawa cikin ƙwarewa.
Hudubar Arfa da ake gabatarwa duk shekara a Dutsen Arafat a lokacin Hajj, na daga cikin manyan hudubobi a Musulunci kuma miliyoyin Musulmi a duniya ke sauraron ta.
A gefe guda kuma, hukumomin Saudiyya sun sake jan hankali ga alhazai da hukumomin ƙasashe masu shiga shirin Hajj da su bi ka’idojin tafiyar Hajj sosai domin tabbatar da tsari da aminci.
Hukumomin sun yi gargadin cewa za a dora alhakin duk wani kuskure na gudanarwa a kan hukumomin ƙasashen da ke da alhakin alhazan su idan aka gaza wayar da kai da kuma daidaitawa yadda ya kamata.
An kuma bukaci a kara wayar da kai musamman kan muhimmancin tafiyar alhazai cikin rukuni ƙarƙashin jagororin da aka ware, domin rage batun ɓacewar mutane da matsalolin gudanarwa a wuraren ibada.

