Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), kuma mamba a Kwamitin Gudanarwa na Kasa na jam’iyyar, Kenneth Okonkwo, ya yi kakkausar suka ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana gwamnatin sa a matsayin “gwamnatin bala’i” sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, karuwar rashin tsaro da kuma hauhawar bashin kasa.
Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Inside Sources with Laolu Akande na gidan talabijin na Channels Television, inda ya yi dogon bayani kan yadda yake kallon gwamnatin Tinubu bayan kusan shekaru uku da hawa mulki.
Lauyan kuma ɗan siyasar adawar ya ce dole ne ‘yan Najeriya su fuskanci hakikanin halin da ƙasar ke ciki, yana mai cewa gwamnatin ta kawo wa al’umma wahala fiye da fata.
“Da farko dai mu kasance masu gaskiya, shekaru ukun nan shekaru ne na bala’i,” in ji Okonkwo.
Ya zargi Shugaba Tinubu da gaza cika alkawuran da ya ɗauka wa ‘yan Najeriya, yana mai cewa abin da kawai shugaban ya cika shi ne yawan bashin da ya ce zai karɓa a kasafin kuɗi.
“Abin da kawai zan iya yarda Shugaba Tinubu ya cika shi ne duk kuɗaɗen bashin da ya ce zai karɓa a kasafin kuɗi, ya karɓo su. Wannan ne kawai ya cika,” in ji shi.
Okonkwo ya kuma soki yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da bashin ƙasa, yana zargin gwamnati da amfani da ma’aunin tattalin arziki na yaudara yayin da ƙarfin samar da kayayyaki a ƙasar ke ci gaba da rauni.
A cewarsa, ƙasar da ba ta dogara da samar da kayayyaki ba bai kamata ta riƙa auna dorewar bashinta ta hanyar GDP kawai ba, yana gargadin cewa hakan na iya jefa Najeriya cikin matsalar tattalin arziki.
“Gwamnatin da ba ta samar da komai yanzu tana lissafa bashinmu ta hanyar GDP cikin salon da ba daidai ba,” in ji shi.
“Duk ƙasar da ba ta samar da kayayyaki yadda ya kamata ba, dole ne ta danganta bashinta da kuɗaɗen shigar ta, in ba haka ba za ta shiga matsala. Nan gaba za mu iya faɗawa matsananciyar matsalar kuɗi.”
Tsohon kakakin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa ya bayyana cewa yanayin kasuwanci a Najeriya ya yi muni matuƙa, yana mai cewa sai mutum ya kasance attajiri mai dala kafin kasuwancinsa ya iya rayuwa a ƙasar.
“Sai ka zama biliyane a dala kafin kasuwancinka a Najeriya ya iya tsira,” in ji Okonkwo.
Ya kuma yi zargin cewa siyasa ce kaɗai kasuwancin da ke bunƙasa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ana karkatar da dukiyar jama’a domin shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.
“Wannan gwamnati ce ta bala’i. Kasuwancin da ke tafiya kawai shi ne siyasa,” in ji shi.
Okonkwo ya kuma yi zargin cewa gwamnoni sun fara ware makudan kuɗaɗe domin tallafa wa yakin neman zaɓe, yana mai cewa gwamnatin na son kawar da duk wata gasa mai ƙarfi a zaɓen 2027.
“Gwamnoni sun riga sun ware Naira biliyan 800 domin tallafa wa yakin neman zaɓe. Wannan ne kawai masana’antar da ke bunƙasa a ƙarƙashin Tinubu saboda ba ya son wata gasa a 2027,” in ji shi.
Dangane da matsalar tsaro, jigon na ADC ya ce Najeriya ta shiga wani mawuyacin hali na kashe-kashe, ta’addanci da asarar rayuka.
“Najeriya ta zama filin kashe-kashe,” in ji Okonkwo.
Ya ƙara da cewa matsayar Najeriya a jerin ƙasashen duniya masu fama da ta’addanci na nuna girman matsalar da ƙasar ke ciki.
“Akwai ƙasashe 195 a duniya, kuma Najeriya ita ce ƙasa ta huɗu mafi fama da ta’addanci,” in ji shi.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, bashin ƙasa, hauhawar farashi, sauyin canjin kuɗi da kuma matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.
Yayin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da kare manufofinta na tattalin arziki a matsayin matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin samun daidaito na dogon lokaci, ‘yan adawa irin su Okonkwo na ganin cewa manufofin sun ƙara talauci, sun raunana kasuwanci tare da jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali saboda tsadar rayuwa.
Labari: Channels tv

