Category: Politics
Zaben 2027: Ina Cikin Shiri Na Korar Tinubu Daga Ofis – Tambuwal
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa yana cikin cikakken shiri tare da shugabannin adawa domin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar ofis ta hanyar dimokuraɗiyya da doka. Tambuwal ya bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Juma’a. “Ina…
Atiku Ya Soki Tursasawa wa El-Rufai da Shugabannin ADC a Kaduna
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, tare da shugabannin jam’iyyar ADC, hari kan tsohon Babban Lauyan Ƙasa Abubakar Malami, da kuma tarwatsa zaman Katsina Elders Forum kan batun tsaro a matsayin “tsari mai…
Yaudara da cin Amana Shi ya Mamaye Siyasar Najeriya – Jonathan
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana siyasar Najeriya a matsayin mai cike da masu cin amana da kuma masu yaudara. “A Najeriya da wuya ka ga mutum ɗaya ya faɗi abu ɗaya da safe ya kuma tsaya a kai da yamma,” in ji shi a jiya. Jonathan ya yi wannan jawabi ne a wurin…
Tsohon Ministan Sufurin Sirika, Ya Nesanta Kansa da Kungiyar Hadin Kan ADC
Hadi Sirika, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, a ranar Laraba ya karyata rahotannin da ke alakanta shi da wata kungiyar adawa da ake cewa tana shirin hambarar da Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027. Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels TV,…
Zaben 2027: Sanata Kabiru Marafa Yayi Alwashin Rage Kuri’un Tinubu
Tsohon Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin rage wa Tinubu ƙuri’u masu yawa a zaɓen 2027. Marafa, wanda a baya-bayan nan ya sanar wa BBC ficewarsa daga jam’iyyar APC, bayan ya zargi Tinubu da ”watsar da shi bayan cin zaɓe” ya ce sai ya kawo wa…
2027: Gungun CPC Za Su Mara Wa Tinubu Baya – Abbas
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya jagoranci haɗa kan tsoffin ‘ya’yan jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) da ke cikin jam’iyyar APC domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027. Abbas, wanda aka fara zaɓar sa a Majalisar Wakilai a shekarar 2011 a ƙarƙashin tutar CPC, ya bayyana cewa gungun na nan…
Zaben 2027: Na Hango Tinubu na Uku Zai Zo – El-Rufai
Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai zo na uku ne a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 mai zuwa. El-Rufai jigo a jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa Tinubu zai sha kashi a zaɓen 2027 idan ya tsaya takara, inda ya ce mafi yawan abin da zai samu shi…
Kakakin jam’iyya: ADC Ta Nesanta Kanta da Bolaji Abdullahi
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tsohon Ministan Wasanni, Bolaji Abdullahi, ba shi da wani matsayi na kakakin jam’iyyar ko sakataren yaɗa labarai, kamar yadda ya ke ikirari. A wata sanarwa da Dr. Christopher O. Okechukwu, Daraktan Harkokin Watsa Labarai na ofishin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya fitar a ranar Alhamis, ADC ta…
2027: Zan Nemi Takarar Shugabancin Ƙasa a Jam’iyyar ADC — Amaechi
Tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sake jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC). Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin tattaunawa da ‘yan jarida a jihar Kano, bayan ganawarsa da gamayyar ‘yan kasuwa. Tsohon Ministan ya jaddada…
Zaben 2027: kowa Yana da Daman Tsayawa Takarar Shugaban kasa – APC
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa ba za ta bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tikitin kai-tsaye na neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, duk da cewa ya riga ya samu amincewar jam’iyyar a matsayin ɗan takarar ta. Suleiman Argungu, Sakatare na Ƙasa mai kula da Ƙungiyoyi (National Organising Secretary),…

