Trends

Jagoranci ADC: INEC ta Amince da Sanata David Mark

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da sabon shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) karkashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.

Batun shugabancin jam’iyyar ya jawo cece-kuce tun bayan da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, tare da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar suka shiga jam’iyyar ADC ta hanyar haɗin gwiwa.

Duk da cewa shugabancin jam’iyyar da mai magana da yawunta, Mallam Bolaji Abdullahi, suka ce babu abin da zai tayar da hankali, wasu ‘yan Najeriya sun nuna damuwa kan lamarin.

A makon da ya gabata, wasu mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) sun kai ziyara ofishin INEC domin tattaunawa kan rikicin shugabancin.

Bayan ganawar, Abdullahi ya shaida wa manema labarai cewa an yi taron ne cikin lumana, inda ɓangarorin biyu suka fahimci juna tare da yarda kan abin da ya kamata a aiwatar.