Dole In Nemo Hakkin Mutanen da aka Kashe a Mangu – Uba Sani

Sanata Uba Sani Gwamnan Jihar kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa ba zai huta ba har sai ya tabbatar da cewa an samu adalci ga matafiya da aka kashe a ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato a lokacin da suke kan hanyar zuwa biki.

Gwamnan ya ce Allah ya dora masa nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma wannan alhakin zai ci gaba da yi har sai ya kammala.

Uba Sani ya yi wannan jawabi ne a Unguwan Dantsoho, Sabon Gari ward, ƙaramar hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, inda ya kaddamar da aikin gina sabuwar hanya daga Hunkuyi Junction zuwa Bassawa, wacce za ta haɗa ƙananan hukumomin Kudan da Sabon Gari.

A tuna cewa a watan Yuni da ya gabata, wasu matafiya 13 daga Jihar Kaduna sun gamu da ajalinsu a hannun wasu ‘yan tawaye a Mangun, yayin da suke kan hanya zuwa bikin aure a ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato. Cikin waɗanda suka mutu, 11 daga cikinsu ‘yan asalin Unguwan Dantsoho ne.

Gwamna Uba Sani ya tuna cewa tun da farko ya yi alkawarin ba da tallafin kuɗi da kuma samar da gidaje ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, kuma ya tabbatar da cewa ya cika wannan alkawari.

Ya ƙara da cewa a lokacin da ya je ta’aziyya, mutanen yankin sun koka da rashin hanya, shi ya sa yanzu yake kaddamar da aikin gina hanyar mai tsawon kilomita 6.

Ya bayyana cewa ƙaramar hukumar Kudan tana daga cikin ƙananan hukumomi 12 da ba su amfana da aikin gina hanya ba cikin shekaru 12 da suka wuce, yana mai cewa ‘yan siyasar yankin ya kamata su ji kunya.

Haka kuma, Gwamnan ya yi alkawarin gina asibiti a Unguwan Dantsoho nan ba da jimawa ba, tare da ba mata tallafin kuɗi don inganta rayuwarsu.

Ya ce: “Wasu ‘yan siyasa sun saba fitowa a talabijin suna ikirarin cewa gwamnatinsu ta tara biliyoyi, amma babu wani abin da ake iya gani a zahiri. Mu ba gwamnati ce ta masu hayaniya ba. Tun lokacin da na hau kujerar mulki, na yi alkawarin kai ci gaba birane da karkara, domin kudaden shiga na Kaduna ba na mazauna birane kaɗai ba ne.”

Gwamna Uba Sani ya yabawa al’ummar yankin bisa zaman lafiya, yana roƙonsu da su ci gaba da rike wannan hali domin ci gaba zai yiwu ne kawai idan an samu zaman lafiya.