NUPENG Ta Janye Yajin Aiki Bayan DSS ta Sasanta su da Kamfanin Dangote

Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas na Najeriya (NUPENG) ta janye yajin aikin da ta fara a faɗin ƙasa bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote Group.

Yajin aikin, wanda ya fara ne a ranar Litinin, ya samo asali ne daga ƙin amincewar kamfanin da ma’aikatansa su shiga cikin ƙungiyar.

An kawo ƙarshen yajin aikin ne bayan taron sulhu da Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS) ta jagoranta.

Taron ya haɗa da Ministocin Ƙwadago da Harkokin Kuɗi, jami’an Hukumar Kula da Tsakanin Samar da Man Fetur da Rarrabawa (NMDPRA), tare da tawagar shugabannin kamfanin Dangote ƙarƙashin jagorancin Seyu Dantata.

Ko da yake ba a bayyana cikakken yarjejeniyar da aka cimma ba, majiyoyi sun tabbatar da cewa an kai ga matsaya ta sulhu wacce ta sa aka dakatar da yajin aikin.