Majalisar Wakilai Ta Ba Ministan Sufurin Sa’o’i 48 Ya Bayyana Gabanta

Kwamitin Majalisar Wakilai na harkokin sufurin ƙasa ya ba Ministan Sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali, wa’adin sa’o’i 48 ya bayyana a gaban kwamitin kan hatsarin da ya rutsa da jirgin ƙasa daga Kaduna mai ɗauke da fasinjoji 618.

Kwamitin ya bayar da wannan umarni ne a ranar Talata bayan Ministan ya kasa halartar zaman binciken da aka shirya, abin da ‘yan majalisa suka bayyana a matsayin raini ga al’ummar Najeriya.

Shugabar kwamitin, Hon. Blessing Onuh, ta nuna ɓacin ranta kan rashin halartar Ministan, inda ta ce abin ba zai taɓa karɓuwa ba.

Ta ce: “Ba a ga kurma rana sai da dalili. Muna hutu amma muka katse hutunmu muka fito daga Lagos saboda wannan bala’in ƙasa, amma sai Minista ya raina majalisa. Wannan ba abin dariya ba ne. Rayukan ‘yan Najeriya sun shiga haɗari. Don haka muna dakatar da wannan zaman har sai Minista ya bayyana a nan cikin sa’o’i 48.”

Mataimakin mai magana da yawun majalisar, Hon. Philip Agbese, ya yi tsokaci cikin tsauri, inda ya bayyana halayyar Ministan a matsayin rashin ƙwarewa da rashin kulawa ga ‘yan ƙasa.

Ya ce: “Wannan aiki na nuna karara cewa bai cancanci muƙamin da Shugaba ya ba shi ba. Yana nuni da cewa bai damu da rayukan ‘yan ƙasa ba, kuma yana cutar da martabar wannan gwamnati. Shugaban ƙasa ya gargadi Ministoci kada su raina majalisa. Amma wannan Minista ya zaɓi raini. Idan bai bayyana ba, to ‘yan Najeriya su sani cewa babu Ministan Sufuri a ƙasar nan.”

A nasa bangaren, wani ɗan kwamitin, Hon. Cyril Hart, ya nuna takaici cewa Alkali wanda tsohon ɗan majalisa ne, ya ƙi girmama gayyatar majalisa.

Ya ce: “Fiye da ‘yan Najeriya 618 na iya rasa rayukansu. Wannan ya nuna akwai matsala mai tsanani a tsarin layin dogo. Tsohon ɗan majalisa bai kamata ya raina wannan kwamitin ba. Hakan cin amana ne ga mutanen da ke neman amsoshin gaskiya. Ko ma MD na Railway ya taɓa neman zama ɗan majalisa, don haka ya san irin girmamawar da ake bin majalisa.”

Kwamitin ya dakatar da zaman binciken har sai Ministan ya bayyana da kansa, tare da gargadin cewa duk wata raini na gaba za a kai shi kai tsaye gaban Shugaban Ƙasa.