Sauraron Tattaunawa: Hukumar Tsaro DSS ta Maka Nasir el-Rufai a kotu

Mallam Nasir El-Rufai Tsohon gwamnan Kaduna

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Department of State Services (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, a gaban kotu bisa zargin “sauraron” tattaunawar wayar Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).

Ana tuhumar tsohon ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) da laifuka guda biyar a cikin sabuwar tuhuma da aka gabatar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A lokacin da aka fara shari’ar a ranar Alhamis, lauyan masu gabatar da ƙara ya sanar da kotu cewa an gyara tuhumar daga laifuka uku zuwa biyar.

Saboda haka, mai shari’a Joyce Abdulmalik ta soke tsohuwar tuhuma.
El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen guda biyar da ake yi masa.

Bayan ya musanta laifukan, lauyan DSS, Oluwole Aladeloye, ya roƙi kotu da ta sanya ranakun fara shari’a. Sai dai lauyan wanda ake ƙara, Oluwole Iyamu, ya nuna adawa, yana mai cewa yana buƙatar ganawa da wanda yake karewa domin ya shafe lokaci a hannun hukumomin tsaro daban-daban.

Iyamu ya shaida wa kotu cewa sun riga sun gabatar da buƙatar beli tun ranar 17 ga Fabrairu, kuma kwanan nan sun ƙara gabatar da ƙarin takardu (further affidavit).

Sai dai mai shari’a Abdulmalik ta ce ba ta ga wannan ƙarin takarda a cikin kundin shari’arta ba, tana mai cewa ya kamata lauyan ya tabbatar da cewa an gabatar da takardun yadda ya dace, maimakon abin da ta kira “wasan kwaikwayo irin na Nollywood” da ke tattare da ɗaukar hotuna a cikin kotu.
Lauyan wanda ake ƙara ya musanta cewa shi ne ya gayyaci masu ɗaukar hoto.

Daga nan sai mai shari’a ta dakatar da shari’ar na ɗan lokaci domin a warware batun ƙarin takardar da aka ce an gabatar.

A tuna cewa a watan Fabrairu, yayin wata hira a shirin talabijin na ‘Prime Time’, el-Rufai ya ce wani ya yi kutse cikin wayar Ribadu, lamarin da ya ba shi damar jin yadda NSA ke bai wa jami’an tsaro umarnin kama shi.

A cewarsa: “Ya yi kiran ne saboda mun saurari kirayensu. Gwamnati na tunanin ita kaɗai ke sauraron kira, amma mu ma muna da hanyoyinmu. Ya yi kiran kuma ya bayar da umarni.”

Ya ƙara da cewa: “Wani ne ya shiga cikin wayarsa. Gwamnati tana sauraron kiranmu koyaushe ba tare da izinin kotu ba. Wani ya shiga wayarsa ya kuma sanar da mu cewa ya bayar da umarnin a kama ni.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *