Hukumar tsaro ta farin kaya, Department of State Services (DSS), ta roƙi babbar kotun tarayya da ta ɓoye sunayen shaidu biyu da ake sa ran za su bayar da shaida a shari’ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai.
A ranar Alhamis ne aka gurfanar da el-Rufai bisa sabuwar tuhuma mai ƙunshe da laifuka guda biyar dangane da zargin shiga cikin tattaunawar wayar Nuhu Ribadu, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ba tare da izini ba. Ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Bayan an karɓi amsar sa, lauyan DSS, Oluwole Aladeloye, ya nemi kotu ta ba da umarni da zai bai wa shaidun damar bayar da shaida da sunayen ɓoye tare da yin hakan ba tare da jama’a sun halarta ba.
Aladeloye ya bayyana cewa wannan mataki na da muhimmanci domin tsaro, yana mai cewa shaidun da iyalansu na iya fuskantar barazana daga mutanen da ke goyon bayan wanda ake ƙara.
Sai dai lauyan el-Rufai, Oluwole Iyamu, ya yi adawa da wannan buƙata.
Iyamu ya shaida wa kotu cewa kundin tsarin mulki ya bai wa wanda ake tuhuma haƙƙin sanin waɗanda ke ba da shaida a kansa. Ya ƙara da cewa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da wata hujja da ke nuna cewa el-Rufai na da barazana ko kuma yana da magoya baya da za su iya cutar da shaidu ba.
Ya kuma yi gargaɗi cewa amincewa da ɓoye sunayen shaidu na iya cutar da shirin kare wanda ake ƙara.
Har ila yau, ɓangaren kariya ya roƙi kotu ta tilasta wa DSS gabatar da hujjojin shari’a domin su samu damar shirya kansu yadda ya kamata.
Sai dai DSS ta yi adawa da wannan buƙata, tana mai cewa takardun da ake nema ba su cikin abubuwan da ta riga ta gabatar a gaban kotu ba.
Iyamu ya kuma sanar da kotu cewa wanda yake karewa ya shigar da ƙara domin a soke tuhume-tuhumen da ake yi masa.
A martani, masu gabatar da ƙara sun ce sun riga sun gabatar da rubutacciyar hujja suna roƙon kotu da ta yi watsi da buƙatar, saboda babu inganci a cikinta.
Haka kuma, el-Rufai ya shigar da buƙatar beli, wadda DSS ta ce ba za ta yi adawa da ita ba.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranakun 18, 19 da 20 ga watan Mayu domin sauraron dukkan buƙatun da ke gaban ta.



