Wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin wucin-gadi da ya hana tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, kiran kansu a matsayin Shugaban Kasa da Sakataren Kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Umarnin kotun da aka bayar a ranar Alhamis ya kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta dakatar da amincewa da Mark da Aregbesola – har ma da duk wani abokin tafiyarsu da ke aiki a ƙarƙashin wannan ikirari – har sai an saurari karar da aka riga aka shigar a kan lamarin.
Nafiu Bala Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC na kasa, ne ya shigar da karar. Ya kalubalanci amincewar INEC da sabuwar shugabancin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar na gaskiya.
A kwanakin baya ne INEC ta sabunta bayananta na hukuma tare da bayyana Mark da Aregbesola a matsayin mambobin sabuwar Kwamitin Aikin Kasa (National Working Committee) na jam’iyyar. Wannan sauyi ya biyo bayan rusa tsohon kwamiti da Chief Ralph Nwosu ya jagoranta a taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 99 da aka gudanar a Abuja.

