Trends

El-Rufai Ya Rubuta Wa Hukumar PSC, da a Binciki Jami’an ‘Yan Sanda Na Kaduna

Nasir El-Rufai Tsohon Gwamnan Kaduna

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) kan abin da ya bayyana a matsayin rashin kwarewa, amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba, da kuma take dokar aikin ‘yan sanda da wasu jami’an rundunar ‘yan sanda ta Kaduna ke yi.

Wannan ƙorafi ya zo ne bayan harin da aka kai a wajen taron kwamitin mika mulki na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Kaduna, inda ake zargin wasu ‘yan daba da kutsa wa, suka lalata kadarori tare da barin mutane da dama da raunuka.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro da ke wurin sun tsaya suna kallo ba tare da sun yi wani yunkurin shawo kan lamarin ba abin da El-Rufai ya ce ya zama al’ada tun zuwan sabon kwamishinan ‘yan sanda a jihar a ranar 30 ga Disamba, 2024.

A cikin ƙorafinsa zuwa PSC, El-Rufai ya gabatar da cikakken bayani kan matsalar tare da neman a gudanar da bincike na gaggawa, mai zaman kansa, da kuma zurfi kan abin da ya kira “ayyuka na ƙarya da kuma sabawa kundin tsarin mulki” da kwamishinan ‘yan sanda da wasu jami’an ke aikatawa.

Ya bayyana cewa tun da farko ya riga ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda game da “ayyukan haramtattun wasu jami’ai” a Kaduna kafin ya ɗaga batun zuwa ga hukumar.

A cikin wasiƙar ƙorafin da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya sanya wa hannu, El-Rufai ya ce:

“Ina rubutawa ne saboda damuwa cewa rundunar ‘yan sanda ce kaɗai cibiyar aiwatar da doka da muke da ita. Dukkan ‘yan ƙasa suna da nauyin ba wai kawai su tallafa mata ba, har ma da tabbatar da cewa hukumar tana da damar amfani da ikon da doka ta ba ta domin ɗaukar matakan ladabtarwa da kuma inganta ɗabi’a a cikin rundunar a kowane lokaci.”

Ya ƙara da cewa hakan ba zai tabbata ba sai idan aka riƙa ja hankalin hukumar kan “ayyukan rashin gaskiya da wasu jami’an da ke bauta wa wasu sha’awoyi na daban, maimakon abin da doka ta tanada a Sashe na 4 na Dokar ‘Yan Sanda, 2020.”

Ƙorafin na zuwa ne a tsakiyar rikicin siyasa da ke ƙara tashi tsakanin El-Rufai, ADC, da kuma rundunar ‘yan sanda.

A ranar 4 ga Satumba, rundunar ‘yan sanda ta Kaduna ta rufe sakatariyar ADC a Kaduna sannan ta gayyaci El-Rufai da wasu shugabannin jam’iyyar shida zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin amsa tambayoyi kan zargin haɗin baki, tayar da zaune tsaye da kuma tada fitina.

Wannan ci gaban ya haifar da suka daga El-Rufai, wanda ya bayyana matakin a matsayin sabawa kundin tsarin mulki, tare da yin rantsuwa cewa zai kai ƙarar har zuwa kotun koli idan ya zama dole.