DSP Adama Adekunle Emmanuel, jami’in Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Abubuwa (NSCDC), an ruwaito cewa abokin aikinsa ya harbe shi har lahira a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar Litinin a wani otal da ke unguwar Life Camp a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Matar mamacin, Hajiya Titilayo Adams, ta shaida wa manema labarai cewa iyalinsa suna zargin akwai “mummunan boye-boye” a cikin al’amuran da suka haifar da mutuwar mijinta.
“A jikinsa mun ga raunukan harsashi a kafadarsa. Ba wani alamar da za a iya cewa harbin bazata ne. A gaskiya suna son rufe abin da ya faru,” in ji ta.
Ta kara da cewa an kai gawar marigayin Asibitin Gwamnati na Maitama ba tare da amincewar iyali ba.
A cewarta, marigayin ya kasance yana aikin tsaro da wani ɗan siyasa a yankin Life Camp, inda ya fita daga gida a ranar Lahadi, 31 ga Agusta, da niyyar dawowa daga baya.
“Ya fita daga gida ranar Lahadi (31 ga Agusta) da niyyar dawowa. Amma daga bisani sai wani abokin aikinsa, wanda ake kira Mr. Emmanuel, ya zo ya shaida mana cewa wai ya harbi kansa da kuskure sau da dama har ya mutu,” in ji ta.
Hajiya Titilayo ta ce sun gano cewa Mr. Emmanuel da ya kawo labarin, ma bai kasance a wurin da lamarin ya faru ba.
“An kira shi kawai aka sanar da shi abin da ya faru. Wannan ya ƙara tabbatar mana da cewa akwai rashin gaskiya a cikin bayanan da ake bayarwa,” in ji ta.
Ta bayyana cewa an ba su rahotanni guda uku masu karo da juna kan abin da ya faru:
- Cewa yayin gyaran bindigarsa ya harbi kansa da bazata.
- Cewa abokin aikinsa ya harbe shi a kuskure.
- Cewa ya harba sama, harsashin ya dawo ya same shi.
Ta yi korafi cewa har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma daga NSCDC, duk da alkawarin da aka yi musu.
“Sun ce za su zo su gan mu, amma har yanzu babu wanda ya tuntube mu. Mijina ya bar iyaye, da ’ya’ya biyu da ya kamata su koma makaranta yau. Har ma kudin haya na gidanmu ya kare. Ni ba ni da aikin da zan iya ciyar da yara. Ina rokon a yi adalci, kuma su taimaka mana wajen daukar dawainiyar jana’izar mijina,” in ji ta cikin kuka.
Yayin da ake ƙoƙarin samun karin bayani, ba a samu amsa daga mai magana da yawun NSCDC reshen FCT, Monica Ojobi, ba, domin saƙonnin da aka tura mata ba a mayar da martani ba.
Haka kuma, lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta FCT, Josephine Adeh, ta ce:
“Zan bincika don tabbatarwa da samun ƙarin bayani kafin in dawo da martani, don Allah ku yi hakuri.”
