ICPC na Neman Ci Gaba da Tsare El-Rufai Har watan Yuni

Mallam Nasir El-Rufai Tsohon gwamnan Kaduna

Wata kotun jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Darius Khobo ta gaza amincewa da buƙatar beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gabatar.

ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu bisa sabbin tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin rashawa da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.

El-Rufai ya bayyana a gaban kotu makon da ya gabata domin sauraron buƙatar belinsa, amma mai shari’a Khobo ya ɗage shari’ar zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani kotun tarayya da ke Kaduna ta riga ta bayar da beli ga El-Rufai a wata shari’a daban da ICPC ta shigar, inda Mai shari’a Rilwanu Aikawa ya amince masa da beli na Naira miliyan 200.

Sai dai kotun ta umarci cewa ya ci gaba da kasancewa a tsare har sai ya cika sharuddan beli, ciki har da hana shi yin magana a bainar jama’a kan shari’ar da kuma wajabcin halartar duk zaman kotu.

Bayan zaman kotu, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan, ya ce an sake ɗage shari’ar, yana mai nuna rashin jin daɗi kan yawaitar dage shari’o’i, inda ya zargi cewa lamarin na da alaƙa da siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *