Trends

Basussukan Najeriya Sun Yi Kamari, Dole Mu Guji Cin Bashi Marar Hankali – Abbas

Abbas Tajudeen kakakin Majalisar Wakilai

Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana damuwa kan yadda basussukan Najeriya ke kara yawa ba tare da tsari ba, yana mai gargadin cewa sun wuce kima bisa doka kuma hakan na barazana ga dorewar tattalin arziki.

Da yake jawabi a wurin taron shekara-shekara na 11 na Kungiyar Kwamitocin Lissafin Kudi na Jama’a ta Yammacin Afirka (WAAPAC) a majalisar dokoki ta tarayya, Abbas ya ce basussukan Najeriya sun kai “matakin da ya yi matukar hatsari,” don haka akwai bukatar gaggawa wajen gyara yadda ake ci da bashi da kuma karfafa kulawa.

A cewar alkaluman kwata na farko na shekarar 2025, jimillar bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39 (kimanin dala biliyan 97), wanda ya ninka daga Naira tiriliyan 121.7 a shekarar da ta gabata. Haka kuma, adadin bashin ya kai kashi 52% na GDP, wanda ya wuce iyakar kashi 40% da doka ta amince da shi.

Abbas ya bayyana wannan matsayin a matsayin “alamar tangarda ga dorewar tattalin arziki,” yana mai kira da a samar da karfin kulawa, gaskiya a harkar cin bashi, da tabbatar da cewa kowanne naira da aka ci da bashi ya samar da amfanin tattalin arziki da na jama’a.

Ya yi kashedi cewa kasashe da dama a Afirka sun riga sun shiga mawuyacin hali na yawan bashi, inda ake kashe kudade masu yawa wajen biyan riba fiye da na kiwon lafiya da sauran ayyukan rayuwa.

“Wannan ba kawai matsalar kasafin kudi ba ce, illa ce ta tsarin tattalin arziki baki daya wadda ke bukatar kulawar majalisa da gaggawa,” in ji shi.

Don shawo kan matsalar, Abbas ya sanar da cewa Najeriya na shirye ta jagoranci kafa Tsarin Kula da Basussuka na Majalisun Dokoki a Yammacin Afirka karkashin WAAPAC.

Tsarin zai hada bayanan bashi a yankin gaba daya, ya kafa ka’idojin gaskiya, tare da bai wa majalisu damar samun sahihan bayanai cikin lokaci don sa ido kan yadda ake ci da bashi.

Bugu da kari, Abbas ya ce za a gudanar da shirin horaswa na kasa da kasa ga kwamitocin harkokin kudi da lissafi domin samar da dabarun zamani wajen nazarin dorewar bashi da kuma gano hadarin tattalin arziki.

Ya kara da cewa:

“Cin bashi ya kamata ya zama don gina hanyoyin sufuri, kiwon lafiya, ilimi da masana’antu da za su samar da ayyukan yi da rage talauci. Amma bashin da ake ci don cin hanci ko alfahari ba za a lamunta da shi ba.”

Abbas ya sake jaddada kudirin Majalisar Wakilai ta 10 wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana, inda ya bayyana cewa karkashin manufar Open Parliament, duk manyan shawarwarin bashi za a gudanar da su a bainar jama’a, sannan kuma za a samar da rahotanni masu sauki da ‘yan kasa za su iya fahimta.

Taron na WAAPAC ya tattaro ‘yan majalisu daga kasashen Yammacin Afirka, abokan cigaba da kuma kwararrun kudi, tare da taken: “Karfafa Ikon Majalisa Kan Kulawa da Basussuka: Rawar Kwamitocin Kudi da Lissafin Jama’a.”

Abbas ya bukaci mahalarta taron da su dauki tattaunawar da muhimmanci, yana mai cewa sakamakon taron zai taimaka wajen karfafa dorewar tattalin arziki da rikon amana a nahiyar.