Category: Politics
2027: PDP ta Amince Kujerar Shugaban ƙasa ta Tafi Kudu
Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya fito daga taronsa na 102 a ranar Litinin, inda ya amince da baki ɗaya cewa takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar za ta tafi Kudu. Wannan matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin rarraba madafun iko na jam’iyyar da gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ke…
Mambobin APC da Dama sun Koma ADC a Sokoto
Wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Gada, jihar Sokoto, sun fice daga jam’iyyar tare da komawa African Democratic Congress (ADC), bisa rashin gamsuwa da ayyukan gwamnatin jam’iyyar mai mulki. An karɓi waɗannan sababbin mambobin ne a hukumance daga hannun Sanata Abubakar Gada, wanda ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wani…
Zaben 2027: Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027. Atiku ya bayyana haka ne ta bakin daya daga cikin masu magana da yawunsa a zaben shugaban kasa na 2023, Tunde Olusunle, a wata hira da jaridar ThisDay. Olusunle ya ce Atiku zai sake tsayawa takara a…
Hon. Emberga ya Gaji Dajoh a Matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue
Hon. Berger Alfred Emberga ne aka zaɓa sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue. Zabensa ya biyo bayan murabus ɗin da tsohon kakakin, Hon. Hyacinth Dajoh, ya yi ta hanyar miƙa wasiƙar da ya rubuta da hannunsa ga Magatakardar majalisar a ranar 24 ga Agusta, 2025. A zaman gaggawa da aka gudanar ranar Lahadi, 25 ga…
Kalu zai Nemi Shugabancin Majalisar Dattawa a 2027 – Cewar Jigo a APC
Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Edward Okocha, ya bayyana cewa Sanata Orji Uzor Kalu na da cikakken shiri da matsayin da zai tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa a shekarar 2027, tare da yin kira ga tsohon mataimakin gwamnan Jihar Abia, Ude Oko Chukwu, da ya janye burinsa na neman kujerar sanata. Chukwu, wanda…
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue ya yi Murabus
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue, Hyacinth Aondona Dajoh, ya ajiye mukaminsa. Wannan lamari ya faru ne kwana biyu kacal bayan majalisar ta dakatar da wasu yan majalisa guda hudu na tsawon watanni uku bisa abin da takwarorinsu suka bayyana a matsayin shirin jefa zauren cikin rikici. A cikin wasiƙar murabus ɗin da Dajoh ya rubuta…
Dole mu Gudanar da Gangami Taron Jam’iyya – Gwamnonin PDP
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) sun fito daga taronsu a Gusau, babban birnin jihar Zamfara a ranar Asabar, inda suka jaddada aniyar su na ci gaba da gudanar da babban taron zaɓe na kasa da aka shirya a Ibadan, jihar Oyo, ranar 15 da 16 ga…
Baba-Ahmed Ya Soki Kungiyar Hadin Kan ADC
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya soki ƙoƙarin hadin kan jam’iyyun adawa ƙarƙashin jagorancin African Democratic Congress (ADC), yana zargin su da yaudarar ‘yan Najeriya da alƙawuran ceto ƙasa. Da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television, Baba-Ahmed ya ce ƙungiyar, wadda ta…
Wike Ya Mallaka wa APC Tsohon Filin Wasa na Area 10 Dake Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bai wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wani muhimmin ɓangare na tsohon Parade Ground da ke Abuja, inda ya mika wa jam’iyyar mallakar fili na dindindin ba tare da biyan kuɗaɗen biliyoyi da dokoki suka tanada ba. An tsara filin ne tun farko a matsayin wurin gudanar…
ADC Ta Soki Karin Albashin ’Yan Siyasa
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana rashin amincewarta da shirin ƙara albashin manyan ’yan siyasa a Najeriya, tana mai kiran wannan yunkuri “mara hankali” da kuma “cin fuskar talakawan ƙasar nan”. A cewar ADC, Shirin da Hukumar Rabon Kuɗaɗe da Sake Tsara Albashi (RMAFC) ke shirin aiwatarwa zai bai wa shugaban ƙasa, mataimakin shugaban…

