Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya soki ƙoƙarin hadin kan jam’iyyun adawa ƙarƙashin jagorancin African Democratic Congress (ADC), yana zargin su da yaudarar ‘yan Najeriya da alƙawuran ceto ƙasa.
Da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television, Baba-Ahmed ya ce ƙungiyar, wadda ta haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsofaffin gwamnonin Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola, tana “yaudarar ‘yan Najeriya.”
Wannan suka tasa ta zo ne duk da cewa abokin takararsa na 2023, Peter Obi, ya riga ya nuna goyon bayansa ga ƙungiyar kafin zaɓen 2027.
Sai dai Baba-Ahmed ya dage cewa Obi ya kamata ya ci gaba da kasancewa a Labour Party ya kuma tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar.
“Ina cikin Labour Party. Ni mutum ne na Peter Obi. Har yanzu ina son Peter Obi ya dawo Labour Party ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko zai sake yin takara tare da Obi, Baba-Ahmed ya ce:
“Idan har Najeriya tana nan, kuma akwai tsarin zaɓe na gaskiya da za a bi. Soyayyata ga Najeriya ba ta gushewa, kuma zan ci gaba da haɗa kai da mutanen da muke da ra’ayi ɗaya wajen dawo da ƙasar.”
Ya ƙara da cewa banda Obi akwai mutum guda kawai da zai iya yi masa mataimaki, amma bai bayyana sunansa ba.
“Na farko bai ce komai ba. Na biyu kuwa shi ne Peter Obi. Ni ina tare da Peter Obi har sai lokacin da ya yanke shawarar janye kansa,” in ji shi.



