Matsalar Tsaro: Buratai Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ta Rufe Iyakar Ƙasar

Tukur Buratai Tsohon Hafsan sojan Nigeriya

Tsohon shugaban rundunar sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (rtd), ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi la’akari da kakaba dokar kulle a faɗin ƙasar a matsayin wata dabarar magance ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.

Buratai ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira da ya yi da Channels Television, inda ya kwatanta halin da ake ciki yanzu kan rashin tsaro da matsalar cutar COVID-19 da ta addabi duniya a baya.

Ya bayyana cewa idan aka yi irin yadda aka tunkari annobar COVID-19, ta hanyar tattara albarkatu da haɗin kan jama’a, da tuni matsalar tsaro ta ƙare.

Ya kuma kawo misali da yadda ’yan Najeriya suka haɗu wajen taimakawa jihar Borno lokacin ambaliyar ruwa a Maiduguri, yana mai cewa irin wannan haɗin kai zai ƙarfafa yaƙin da ake yi da rashin tsaro.

Wannan shawarar tasa ta zo ne bayan rahoton kwanan nan na Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam (NHRC), wadda ta nuna damuwa kan ƙara ta’azzarar keta haƙƙin rayuwa da ’yanci, inda aka bayyana cewa sama da mutane 50 aka kashe a hare-hare daban-daban cikin mako guda kacal.

Buratai ya jaddada cewa ba aikin sojoji kaɗai ba ne, ya kamata a ɗauki batun tsaro a matsayin matsalar ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar haɗin kai da sadaukarwa daga kowa.

“Lokacin da ake fuskantar matsalar ƙasa, wajibi ne a haɗa kowa, ba sojoji kaɗai ba. Ku duba lokacin COVID-19, kuɗi da albarkatu nawa aka zuba? Aka yi amfani da kafafen yaɗa labarai, tallace-tallace, tallafin palliatives da matakan kariya.

Duk ƙasa an kulle saboda COVID-19. Za mu iya yin haka, mu kakaba dokar kulle a ƙasa gaba ɗaya domin kowa ya maida hankali wajen magance wannan cutar ’yan ta’adda da ’yan bindiga,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tun kafin ya bar ofishinsa a matsayin shugaban sojoji, ya yi gargadi cewa rikicin ’