Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya fito daga taronsa na 102 a ranar Litinin, inda ya amince da baki ɗaya cewa takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar za ta tafi Kudu.
Wannan matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin rarraba madafun iko na jam’iyyar da gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ke jagoranta.
A yayin taron, kwamitin ya gabatar da rahotonsa ga NEC, wanda mambobin suka amince da shi baki ɗaya.
Da yake karanta sanarwar bayan taron ga ’yan jarida da mahalarta, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce NEC ta yanke shawarar ci gaba da tsarin rarraba mulki tsakanin Arewa da Kudu.
Ya kara da cewa, tun da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa zai fito daga Arewa a babban zaɓen shugabannin jam’iyya na ƙasa da aka tsara a gudanar ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan, jihar Oyo, NEC ta amince kujerar shugaban ƙasa ta PDP ta koma ga Kudu.








