Harkokin kasuwancin Najeriya da ƙasashen waje sun ƙara ƙarfi a zangon farko na shekarar 2026, bayan sabbin bayanai daga Nigeria Customs Service (NCS) sun nuna gagarumin ƙaruwa a fitar da kayayyaki, tara kuɗaɗen shiga da kuma jigilar kaya ta tashoshin jiragen ruwa.
Fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje ya ƙaru da kashi 38.68 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci a 2025, inda ya kai dala miliyan 925.84. Haka kuma, adadin kwantena da aka fitar ya kusan ninka sau biyu daga 9,722 zuwa 19,014, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 95.58 cikin 100.
Hukumar ta ce: “Kayayyakin da aka fitar a zangon farko na 2026 sun kai dala miliyan 925.84, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 38.68 idan aka kwatanta da 2025, yayin da jimillar kwantena ta ƙaru zuwa 19,014 daga 9,722, wato ƙaruwa da kashi 95.58.”
Bayanan kowane wata sun nuna bambance-bambance a yanayin ci gaban. A watan Janairu an samu ɗan raguwar kashi 1.12 zuwa dala miliyan 267.66, sai watan Fabrairu da ya farfaɗo da ƙaruwa da kashi 12.43 zuwa dala miliyan 253.12, yayin da watan Maris ya fi kowa ƙarfi da tashin gwauron zabi na kashi 135.83 zuwa dala miliyan 425.48 idan aka kwatanta da bara.
Kuɗaɗen shiga da ke da alaƙa da fitar da kayayyaki su ma sun ƙaru. Kuɗin harajin fitarwa ya tashi da kashi 21.81 zuwa Naira miliyan 199.36, yayin da kuɗin NESS ya ƙaru da kashi 20.15 zuwa Naira biliyan 6.03.
Wannan ci gaban na nuni da inganta ayyukan tashoshin jiragen ruwa, sauƙaƙa harkokin kasuwanci, da kuma ƙoƙarin bunƙasa fitar da kayayyakin da ba na mai ba, musamman a fannonin noma, masana’antu da ma’adinai.
Jami’an kwastam sun bayyana cewa ƙaruwa a zirga-zirgar kwantena na nuna kyakkyawan amfani da kayan aikin tashoshin jiragen ruwa da kuma ingantaccen sarrafa kaya.
Da wannan gagarumin ci gaba na watan Maris ya zama abin koyi, masu ruwa da tsaki sun ce yana da muhimmanci a ci gaba da wannan nasara har ƙarshen 2026, musamman ganin cewa hukumar na hasashen tara Naira tiriliyan 9 a shekarar, bayan ta zarce burinta na Naira tiriliyan 6.5 a 2025.









