Seme Customs Sun Tara Naira Biliyan 9.8 A Cikin Wata Biyu — NCS
Rundunar Seme ta Hukumar Kwastam ta Najeriya Nigeria Customs Service (NCS) ta bayyana cewa ta tara kudaden shiga na Naira biliyan 9.798 tsakanin watan Maris zuwa Mayu 2026, abin da ya nuna gagarumin karuwa idan aka kwatanta da Naira biliyan 2.188 da aka tara a daidai wannan lokaci a shekarar 2025. Kwamandan shiyyar, Abdullahi Kaila,…
