Zaben 2027: Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa – Atiku

Atiku Abubakar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Atiku ya bayyana haka ne ta bakin daya daga cikin masu magana da yawunsa a zaben shugaban kasa na 2023, Tunde Olusunle, a wata hira da jaridar ThisDay.

Olusunle ya ce Atiku zai sake tsayawa takara a 2027 saboda Najeriya tana bukatar a ceto ta daga halin da ake ciki a zamanin mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Wannan martanin na Atiku ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa watakila ya daina takarar bayan wani malamin jami’a daga Achievers University, Farfesa Ola Olateju, ya ce Atiku ya fi mayar da hankali kan gyaran Najeriya fiye da neman mulki.

Sai dai Atiku ya nesanta kansa daga wannan magana, yana mai cewa ba ta fito daga gare shi ba.

“Lokacin da mutane ke wakiltar ni a taruka, muna tattaunawa kan abubuwan da za a fadi. Amma a wannan karon, babu wata magana da aka yi da ni don bayyana ra’ayina. Don haka, Farfesa Olateju bai yi magana a madadina ba,” in ji Atiku daga gidan hutunsa da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Ya kara da cewa: “Zan tsaya takara a 2027. Najeriya tana bukatar a ceto ta da gaggawa daga dakin jinya da aka jefa ta. Lalacewar da ke faruwa a kasar nan, matsanancin talauci da wahala da kunci, ba abin da za a amince da shi bane.”