Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar tarayya, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), jim kaɗan bayan korar da aka yi masa daga jam’iyyar.
A cikin wata doguwar sanarwa da ya fitar ga jama’a, Jibrin ya bayyana matuƙar takaicinsa kan hukuncin da ya kira “mamaki mara daɗi”, yana mai cewa korar da aka yi masa ba ta yi adalci ba kuma an saba ƙa’idojin bin doka da oda.
“Ina da yakinin cewa abinda na faɗa a hirar da na bayar kwanaki kaɗan da suka gabata — a Turance da Hausa — ba su cancanci hukunci mai tsanani irin wannan ba,” in ji shi, yana mai jaddada cewa maganganunsa sun yi daidai da tushen manufofin jam’iyyar da ke ba da dama ga ’yancin faɗin albarkacin baki da bambancin ra’ayi.
Ya kuma ce ba a taɓa gayyatarsa daga kowanne sashen jam’iyyar domin ya yi bayani ko kare kansa kafin a sanar da korar ba, yana mai kiran wannan mataki “take hakkin sauraro da bin doka.”
“Ko a ƙarƙashin mulkin soja, wanda ake zargi ana gurfanar da shi a kotun soja,” in ji shi, yana mai cewa da an bi tsari daidai, da ba a kai ga wannan korar ba.
Duk da haka, Jibrin ya ce yana nan daram a kan akidar siyasa mai zaman lafiya da girmama juna, yana mai cewa da ya fi so ya ci gaba da hidima a cikin NNPP, amma ya karɓi hukuncin jam’iyyar da zuciya ɗaya. Sai dai ya nuna shakku kan ingancin hukuncin, yana zargin cewa wata ƙungiya ce kawai a cikin jam’iyyar ta ɗauki wannan mataki.
“Da ba don girmamawa da nake yi wa jam’iyya, mambobi da shugabanninta ba, da na dauki wannan hukunci a matsayin babu kuma na garzaya kotu,” in ji shi.
Dangane da batun rashin biyan kuɗin jam’iyya, Jibrin ya roƙi a tura masa daftarin biyan kuɗi, yana mai alƙawarin biyan su nan take. Ya kuma roƙi shugabannin NNPP da magoya baya su guji cin mutunci, su kasance cikin ladabi da mutunta juna duk da rabuwa.
“Jam’iyyar NNPP ba ta yarda cewa kowane mutum na da darajar siyasa ba, kuma akasari tana kasa kula da mutane da mutunci. Ina gode wa Allah da irin tasirin da na samu, kuma zan zuba shi a inda za a mutunta shi da ƙima,” in ji shi.
Sai dai duk da koke-koken nasa, Jibrin ya gode wa jam’iyyar bisa goyon bayan da ta ba shi a lokacin da yake cikinta, tare da nuna alfahari da gudunmawar da ya bayar wajen ci gabanta.
Ya ƙare jawabin nasa da kiran magoya bayansa da su biyo shi a sabon tafiyar siyasa da ya fara, yayin da ya yi addu’ar alheri ga waɗanda suka zauna a cikin NNPP. Haka kuma ya bayyana cewa zai ɗauki lokaci kafin ya yanke shawarar jam’iyyar da zai shiga a gaba.
“Allah Ya taimake ni,” in ji shi, yana nuna buɗewar sabon babi a rayuwarsa ta siyasa.
