Mai Gudanar da Lamuran Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (rtd.), ya bayyana cewa ya cika mandatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi bayan ayyana dokar ta-baci a jihar a ranar 18 ga Maris, 2025.
Ibas ya yi wannan jawabi ne bayan kammala zaɓen kananan hukumomi da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta Rivers (RSIEC) ta gudanar, wanda ya ce ya nuna cikakken dawowar mulkin dimokuraɗiyya a matakin ƙananan hukumomi.
Tun a farkon shekarar, Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakinsa da kuma dukan ‘yan majalisar dokoki na jihar lokacin da ya ayyana dokar ta-baci a Rivers, inda ya nada Ibas a matsayin mai gudanarwa guda ɗaya tare da takamaiman umarni: ya daidaita jihar, ya farfaɗo da cibiyoyinta, sannan ya dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya.
Zaɓen da RSIEC ta shirya ya samar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar. A cewar Ibas, zaɓen ya kasance mai sahihanci, gaskiya kuma ba tare da barazana ba, abin da ya bai wa al’ummar Rivers damar bayyana ra’ayinsu cikin ‘yanci.
Ya yaba wa hukumar zaɓe, jami’an tsaro da ma’aikatan jihar saboda samar da yanayi da ya ba da damar aiwatar da abin da ya kira “cikakken aiwatar da umarnin shugaban ƙasa.”
Shugaban RSIEC, Dr. Mike Odey, shima ya bayyana tsarin a matsayin tarihi, inda ya jaddada cewa wannan shi ne karon farko a Najeriya da aka gudanar da dukkan matakan zaɓen kananan hukumomi daga sanarwa har zuwa kaddamarwa cikin kwanaki 30 kacal.
Yayin da dokar ta-bacin watanni shida za ta ƙare a ranar 18 ga Satumba, Ibas ya ce za a fitar da takardar “white paper” bisa ga rahoton RSIEC domin kammala matakan tabbatar da nasarorin da aka samu a karkashin tsarin wucin-gadi.
“An daidaita jihar Rivers, an farfaɗo da cibiyoyinta, kuma an dawo da dimokuraɗiyyar ƙananan hukumomi. Mandatar da Shugaban Ƙasa ya damƙa min ta cika,” in ji tsohon hafsan rundunar sojin ruwa mai ritaya.
