An samu gawar wata daliba mai karatun shekara ta farko a Jami’ar Taraba (TSU), Jalingo, Comfort Jimtop, a gidan saurayinta a cikin yanayi da ba a bayyana ba.
Marigayiyar, wacce ta fito daga Karamar Hukumar Takum a Jihar Taraba, tana karatu ne a Sashen Kwalliya da Hulɗar Jama’a na jami’ar. An gano gawarta ne da yammacin ranar Juma’a.
Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan sanda sun samu kwalaben giya a gefen gadon da aka tsinci gawar dalibar.
An kuma tattaro cewa akwai mutane 15 da ke zaune a gidan da aka gano gawar, amma dukkan su, ciki har da wanda dakinsa aka samu gawar dalibar, sun gudu suka bar gidan.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Taraba, ASP Leshen James, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa saurayin marigayiya, wanda aka gano da sunan Emmanuel Shata, shima dalibi ne a Jami’ar Taraba. Ya ce lokacin da ‘yan sanda suka isa gidan, ba su tarar da kowa a wurin ba.
ASP James ya ƙara da cewa bincike ya na ci gaba, kuma rundunar ‘yan sanda na kan hanyar cafke Shata da sauran mazaunan gidan da suka tsere.
