Trends

Tinubu Ya Soke Harajin Kashi 5% Kan Sadarwar da Intanet

Bola Ahmed Tinubu Shugaban Nigeriya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta soke harajin kashi 5% da ake karɓa a kan ayyukan sadarwa, wanda ya haɗa da kiran murya da amfani da bayanan intanet.

Hukumar Wayar Tarho ta Ƙasa (NCC) ta bayyana hakan ne ta bakin Babban Kwamishinan Hukumar, Dr. Aminu Maida, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin cire harajin yayin tattaunawa kan sabuwar dokar kuɗi.

A cewar Maida, manufar Shugaban ƙasa ita ce kare ‘yan Najeriya daga ƙarin matsin tattalin arziki tare da bunƙasa ci gaban tattalin arzikin dijital a ƙasar. Ya jaddada cewa wannan mataki zai rage kuɗin da ‘yan ƙasa ke biya, wanda zai kawo sauƙi ga fiye da masu amfani da wayar tarho miliyan 171 a fadin ƙasa.

An kafa wannan haraji tun a shekarar 2022 a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, lamarin da ya jawo suka daga masana’antar sadarwa da ƙungiyoyin kare haƙƙin mabukata. Kungiyar masu lasisin kamfanonin sadarwa (ALTON) ta yi gargadin cewa irin wannan nauyi zai iya dakile ci gaban harkar sadarwa a Najeriya, inda ta nuna cewa ƙasar na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da mafi tsananin haraji a fannin sadarwa a Afirka ta Kudu da Sahara.

A lokacin da aka gabatar da shi, gwamnati ta kare wannan haraji a matsayin matakin ƙara samun kuɗaɗen shiga, musamman ganin yadda ragin kuɗin mai ya ke shafar tattalin arzikin ƙasa. Amma, masu suka sun bayyana cewa hakan ya ƙara jefa al’umma cikin ƙuncin rayuwa, musamman duba da hauhawar farashi da kuma karin kuɗin amfani da sabis na sadarwa.