Babban Taron ADC Yana Gudana Cikin Tsauraran Matakan Tsaro
Jami’an tsaro sun kakabawa wajen taron kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Abuja tsauraran matakan tsaro a ranar Talata, yayin da kimanin wakilai 7,000 suka taru domin zaben sabbin mambobin Kwamitin Zartarwa na Kasa (NWC). Jami’an Nigeria Police Force da na Department of State Services sun bazama a kusa da Rainbow Event Centre,…
