World Bank ya bayyana damuwa kan raunin tsarin kula da kudaden gwamnati a Najeriya, yana gargadin cewa gibba a harkokin baitul mali da rahotanni na rage gaskiya da ingancin tafiyar da kudade.
A cikin rahoton sa na watan Afrilu 2026 mai taken Nigeria Development Update, Bankin ya ce harkokin baitul mali har yanzu suna rarrabe, inda kusan asusun TSA guda 5,000 ba su hade gaba daya cikin tsarin kudaden shiga na kasa ba.
Rahoton ya ce, “A karkashin wadannan kalubalen tattalin arziki, akwai matsaloli na tsari da na hukumomi da ke hana cikakken bayyanawa, hada kudade, da kuma ingantaccen sarrafa kudaden gwamnati.”
Ya kara da cewa muhimman sassa kamar na kudaden shiga, kadarori, basussuka, da kuma kula da alkawuran kashe kudi ba su cika aiki yadda ya kamata ba. Haka kuma, dandamalin da hukumomi kamar Office of the Accountant-General of the Federation (OAGF), Debt Management Office (DMO), da Budget Office of the Federation (BOF) ke amfani da su ba su hade juna yadda ya kamata ba, lamarin da ke haifar da gyare-gyare da hannu, jinkiri da rashin daidaito.
Bankin ya kuma nuna matsaloli a bangaren bayyanawa, yana mai cewa Najeriya ba ta fitar da sahihan rahotannin kudi na tarayya da aka tantance ba tun shekarar 2021, yayin da har yanzu ana amfani da tsohuwar dokar duba kudi ta shekarar 1956.
Ya ce, “Jinkirin duba kudi na rage ikon sa ido, yana raunana daukar alhaki, kuma yana takaita damar masu ruwa da tsaki wajen tantance yadda gwamnati ke tafiyar da kudade.”
A gefe guda, an fara wasu gyare-gyare daga ofishin Akanta Janar na Tarayya, ciki har da kaddamar da tsarin Federal Treasury e-Receipt da kuma Revenue Optimisation and Assurance Platform, domin hada tsarin biyan kudi, sarrafa kudaden shiga ta atomatik da kuma toshe gibba.
Bankin ya jaddada cewa magance wadannan matsaloli na tsari yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da daidaiton kashe kudi da kuma karfafa amincewar masu zuba jari. Ya kuma yi gargadin cewa matsin lamba kan kudaden gwamnati na iya karuwa gabanin zaben shekarar 2027, duk da cewa karin kudaden man fetur a 2026 na iya kawo sauki.
Haka kuma ya kara da cewa sabon tsarin haraji na Najeriya da aka fara aiwatarwa a Janairu 2026 ya sabunta dokoki tare da gabatar da harajin mafi karanci na duniya, amma kudaden VAT na iya raguwa a gajeren lokaci kafin a fadada tushe da kuma inganta bin doka.
