Trends

Rashin Inganci da Karancin YasaFetur na Waje Ya Fi Araha – CORAN

Kungiyar masu tace danyen mai a Najeriya, Crude Oil Refiners Association of Nigeria, ta yi watsi da ikirarin cewa fetur da ake shigo da shi daga waje ya fi na cikin gida araha saboda inganci, tana mai cewa bambancin farashin ya samo asali ne daga bambancin inganci.

Sakataren yada labarai na CORAN, Eche Idoko, ya bayyana cewa galibin fetur da ake shigo da shi ana hadawa ne (blending) daga kasashe kamar Kazakhstan da yankin Gabashin Turai, kuma sau da yawa yana cika mafi karancin ka’idoji ne kawai.

Ya ce, “Dangane da inganci, ba za su iya gogayya da fetur din da ake tacewa a matatunmu ba. Hada fetur (blending) ya fi araha fiye da tacewa gaba daya.”

Idoko ya soki World Bank kan rashin yin kwatanci iri daya, yana mai cewa nau’ikan fetur sun bambanta ta fuskar kauri, yanayin kamawa da wuta, da kuma yadda yake daskarewa—abubuwan da ke tasiri kan farashi. “Ya kamata a kwatanta iri daya da iri daya,” in ji shi.

Ya kara da cewa hada fetur ba haramun ba ne, amma yana samar da fetur mai karancin matsayi wanda ke da rahusa. “Yayin da inganci ya karu, farashi ma zai karu. Idan tacewa na rage gurbatar muhalli, to babu shakka zai fi tsada,” ya bayyana.

Har ila yau, ya danganta tsadar fetur a cikin gida da matsalolin samar da danyen mai, yana mai cewa matatun mai, ciki har da Dangote Refinery, na sayen danyen mai a farashi mai tsada ba tare da rangwame ba. “Ba mu samun rangwame. Dangote da sauran matatun na saye daga kasuwannin duniya bisa farashin Brent,” in ji shi.

A baya, World Bank ya bayyana cewa fetur da ake shigo da shi ya fi na Dangote araha da kusan kashi 12, yana mai ba da shawarar a sake bude shigo da fetur domin karfafa gasa. Ya nuna cewa farashin daga matatar Dangote na ₦1,275 a lita ya fi farashin shigo da kaya na ₦1,122 a lita, abin da ke nuna karkacewar kasuwa.

Bayan suka, Bankin Duniya ya fayyace cewa ba ya nufin goyon bayan shigo da fetur gaba daya ba ne, illa dai yana cikin shawarwari na gyare-gyare don inganta gasa da kare masu amfani. Haka kuma ya bukaci a samar da tallafi ga masu karamin karfi.

A halin yanzu, matatar Dangote na samar da sama da kashi 92 na fetur din da ake amfani da shi a Najeriya, bayan da mai kula da bangaren ya dakatar da lasisin shigo da fetur a watan Janairu 2026, lamarin da ya rage kaso na shigo da kaya zuwa kashi 8 kacal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *